Tinubu Ya ba kowace 'Yar Wasa a Tawagar Flamingos Kyautar Naira Miliyan 100

Tinubu Ya ba kowace 'Yar Wasa a Tawagar Flamingos Kyautar Naira Miliyan 100

  • Shugaba Bola Tinubu ya sanar da bayar da kyautar N100m ga kowace ’yar wasan tawagar Flamingos bayan lashe gasar cin kofin duniya
  • Tawagar Najeriya ta doke Japan da ci 2-1, inda ta lashe kofin gasar cin kofin duniya ta maya yan kasa da shekaru 17 da aka gudanar a Morocco
  • Kocin tawagar shi ma zai samu N100m, yayin da kowane mamban tawagar masu horarwa zai karɓi N50m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da bayar da kyautar Naira miliyan 100 ga kowace ’yar wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Flamingos.

Tinubu ya ba yan wasan wannan kyauta ne bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin duniya ta mata ’yan ƙasa da shekaru 17.

Flamingos.
Tawagar yan wasa mata na Najeriya lokacin da suke murnar lashe kofin duniya na yan kasa da shekaru 17 a Morocco Hoto: Super Falcons
Source: Facebook

Flamingos ta lashe kofin duniya

Kara karanta wannan

Maganar zargin kisan Kiristoci ya dawo yayin da zaɓen Najeriya ke ƙaratowa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tawagar Najeriya ta doke Japan da ci 2-1, inda ta lashe kofin gasar cin kofin duniya ta mata ’yan ƙasa da shekaru 17 da aka gudanar a Morocco.

A yau ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba, 2026 ne ’yan wasan da jami’ai masu horar da su suka ziyarci fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Tinubu ya ba kowace yar wasa N100m

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ce ta tarbe du s madadain Shugaba Bola Tinubu, inda ya ta sanar da kyautar a madadin shugaban ƙasa.

Ta ce Najeriya na alfahari da nasarar da tawagar yan wasa mata ta samu, wanda ta kara daga kimar Najeriya a idon duniya a bangaren wasanni.

Oluremi ta bayyana cewa za a ajiye kuɗaɗen a bankunan da aka ware domin kula da su a madadin matasan ’yan wasan.

Kyautar koci da masu horaswa

Baya ga yan wasan tawagar, rahoton ya kuma bayyana cewa kocin tawagar Flamingos zai samu kyautar Naira miliyan 100.

Haka kuma, kowane mamba na tawagar masu horar da ’yan wasan zai karɓi Naira miliyan 50 kyauda daga mai girma shugaban kasa.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262