Bidiyon da aka Nuna Sarki Sanusi II da Wasu Mata Ya Jawo Rudani
- Diyar Sarki Muhammadu Sanusi II, Sabeera Sanusi, ta shirya wani bikin baje kolin kayan sawa da ya kunshi maza da mata
- Bidiyon wata mata da ta cire wani bangare na kayanta yayin da take wajen baje kolin ya jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke ganin bai dace ba
- Sai dai wasu sun bayyana cewa bidiyon ba a dauke shi a gaban Sarki Sanusi II ba, domin matar ta cire kayan ne bayan ya bar wurin taron
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Wani bikin baje kolin kayan sawa da Sabeera Sanusi, diyar Sarki Muhammadu Sanusi II, ta shirya ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.
An gudanar da bikin ne inda maza da mata suka fito kan dandamali domin baje kolin kayan sawa iri-iri, kamar yadda ake yi a wasu kasashen Turai, musamman Faransa.

Source: Twitter
Wani bidiyo da wani mai suna Khalifa ya wallafa a X ya nuna cewa Sarkin da kansa ya halarci taron, amma baya wajen a lokacin da aka yi abin da ya tayar da kura.
Wata ta jawo ce-ce-ku-ce
A wani bangare na bikin, wata mata da ta kammala rangadin nuna kaya a kan dandamali ta cire wani bangare na rigarta a gaban masu kallo.
Lamarin ya haifar da muhawara, inda wasu suka yaba da bikin, yayin da wasu suka soki yadda aka gudanar da shi, suna masu cewa ya saba wa al'adun Hausawa da koyarwar addinin Musulunci.
Karin haske kan bidiyon
Sai dai wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun bayyana cewa bidiyon matar da ta cire kayan ba a dauke shi a lokacin da Sarki Sanusi II yake wurin taron ba.
Wasu sun bayyana cewa an gyara bidiyon ne aka hada wasu hotuna domin a samar da fahimtar cewa matar ta yi hakan ne a gaban Sarkin.
Wasu kuma sun ce matar ta cire kayan ne bayan Sarki Sanusi II ya bar wajen bikin, lamarin da ya sa suka bukaci jama'a su fahimci cikakken abin da ya faru kafin yanke hukunci.

Source: Original
Maganar Abba Hikima
A nasa martanin, Lauya Abba Hikima ya bukaci Sarki Muhammadu Sanusi II, da ya dauki matakin gyara idan har yana wakiltar Musulunci kamar yadda ake fada.
A sakon da ya walllafa a Facebook, ya ce:
"Da dukkan girmamawa, in dai Sarkin Kano Muhammadu Sanusi sarkin Musulunci ne, kuma yana wakiltar Musulunci kamar yadda ake fada, to lallai ya kamata ya yi gyara. Don Allah."
Abba Hikima ya bayyana cewa an tabbatar masa cewa Sarki Sanusi II ya halarci taron amma ba ya nan a lokacin da aka yi abin Allah wadai din.
Sanusi II ya bude masallaci
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya karbi bakuncin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wanda ya jagoranci bude Masallacin Zawiyya da aka sabunta a Gusau, babban birnin jihar.
Babban limamin Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari, shi ma ya halarci taron, inda ya jagoranci sallar Juma'a a masallacin mai dimbin tarihi.
Wasu masu amfani da Facebook sun yaba da aikin sabunta masallacin, yayin da wasu suka yi amfani da damar wajen sukar gwamnatin Zamfara kan matsalar tsaro da ke addabar jihar.
Asali: Legit.ng

