Shugaban APC Ya Shaida wa Atiku Abin da Zai Hana Shi Zama Shugaban Kasa a ADC
- Nentawe Yilwatda bai damu da halin da Atiku Abubakar da sauran ‘yan takaran jam’iyyar ADC suka shiga ba
- Shugaban jam’iyyar APC ya ce ‘dan takaran shugaban kasar da David Mark suka tsaida ba zai yi galaba a kan su ba
- Yilwatda ya yi hujja da cewa ko a baya da Atiku ya yi kokari a zabe saboda ya samu takara ne a inuwar PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Nentawe Yilwatda ya yi tsokaci game da rikicin jam’iyyar ADC da kuma damar da Atiku Abubakar yake da ita a zaben 2027.
Shugaban jam’iyyar na APC a Najeriya bai ganin cewa Atiku Abubakar zai iya yin galaba a kan Mai girma Bola Ahmed Tinubu a takara.

Source: Twitter
Akwai hannun APC a rikicin gidan jam'iyyar ADC?
A wata doguwar hira da aka yi da shi a gidan talabijin Channels, Farfesa Nentawe Yilwatda ya nuna ba su tsoron ADC a zabe mai zuwa.
Shugaban APC na kasa ya bayyana cewa babu abin da ya shafe su da rikicin da ADC ta ke fama da shi a kotu da su Nafiu Bala Gombe.
Ganin kotu ta haramta takarar Atiku da sauran wadanda David Mark ya ba tikiti, Nentawe Yilwatda ya ce matsalar ba ta shafe su a APC ba.
Yilwatda ya kuma bayyana cewa babu hannun jam’iyya mai mulki a wannan tirka-tirka ta kotu, yana cewa matsala ce ta cikin gidan ‘yan ADC.
Shugaban APC: Za mu doke Atiku Abubakar
Shi dai shugaban jam’iyya mai mulki ya ce suna da kwarin guiwar lallasa Atiku Abubakar idan za a fito a yi zabe na gaskiya da adalci a badi.
Farfesan yake cewa ko farin jinin da Atiku ya samu a zabukan baya, a dalilin kafuwar jam’iyyar PDP ba wai saboda yana da karbuwa ba ne.
Shi a karon kan shi Atiku bai da farin jinin lashe zabe a ra’ayin Yilwatda mai jagorantar APC NWC.
“Bai samu kuri’u saboda yana Atiku ba; ya samu ne saboda tsarin jam’yyar PDP.
Jam’iyyar PDP ce ta kawo Atiku, bai wai shi Atiku ne ya yi nasara a karon kan shi ba.
- Nentawe Yilwatda
A tattaunawar da aka yi da shi, Yilwatda ya nuna wannan karo Atiku ba zai samu kuri’u daga yankin Kudu maso kudu ba, akasin zaben 2019.
Ya bada misali da irinsu jihar Osun da mutanen ta suka zabi PDP sosai a takarar 2023, yake cewa wannan karo lamarin ba haka yake ba a ADC.
“Atiku ya taba kasancewa a ADC, me ya tabuka a wancan lokaci? Atiku ya yi takara a wasu wurare, bai yin komai sai yana rike da tutar PDP kuma wannan karo jam’iyyar ba ta nan.”
Bidiyon hirar da aka yi da shugaban APC a shafin hadiminsa, Imran Muhammad a kafar X.
Arewa za ta zabi Bola Tinubu - Abdulaziz Yari
An ji cewa Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce Shugaba Bola Tinubu zai samu nasara a Arewa a zaɓen 2027.
Tsohon gwamnan ya ce Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya yi alƙawarin samar wa Tinubu ƙuri’u miliyan biyu a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya lissafa ayyukan gwamnatin Tinubu a Jigawa, ciki har da tituna, gidaje da tallafin noma da ruwa.
Asali: Legit.ng


