Bidiyon Minista Tana Raba Dauri Daurin N100,000 Ya Tada Kura, Mutane Sun Dura Kanta

Bidiyon Minista Tana Raba Dauri Daurin N100,000 Ya Tada Kura, Mutane Sun Dura Kanta

  • Ministar Harkokin Mata da Ci gaban Al’umma, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bayyana a wani bidiyo tana rabawa mata damin kuɗi da kayan dinki
  • Bidiyon mai tsawon daƙiƙa 45 ya nuna ministar tana raba kuɗi a cikin ambulan masu hotunan Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima
  • Wasu masu amfani da kafar sada zumunta sun yi tambayoyi da suka soki yadda gwamnati ke amfani da kuɗin da aka samu bayan cire tallafin fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria - Ministar Harkokin Mata da Ci gaban Al’umma, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bayyana a wani bidiyo da ya yaɗu sosai a intanet tana rabawa mata ɗauri-daurin kuɗi.

Faifan bidiyon ya ja hankalin yan Najerirya matuka, ganin yadda ministar ta rika faba daurin yan dubu-dubu na N100,000 da kayan ɗinki masu tambarin jam’iyyar APC a wani gangamin siyasa a Jihar Rivers.

Kara karanta wannan

"Ana kewar Buhari": Amaechi ya tuna rayuwa a lokacin tsohon shugaban kasa

Imaan Sulaiman
Ministar Harkokin Mata da Ci gaban Al’umma, Imaan Sulaiman-Ibrahim a ofis a Abuja Hoto: Imaan Sulaiman Ibrahim
Source: Twitter

Bidiyon mai tsawon daƙiƙa 45, an wallafa shi ne a shafin TikTok mai suna Move with Imaan, wanda ke tattara bayanan ayyukan ministar.

Yadda minista ta raba kudi a taron mata

A cikin takaitaccen bidiyon, an ga Imaan Sulaiman-Ibrahim tana miƙa ɗaurin kuɗi da kuma buhun kayan ɗinki masu tambarin APC ga matan da suka halarci gangamin.

Bidiyon ya kuma nuna ministar tana raba kuɗi a cikin ambulan masu hotunan Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima.

An ga kowace mace tana karɓar daurin takardun kuɗi na N1,000, wanda wasu ke ganin kowane dauri ya kai N100,000.

Martanin wasu yan Najerirya

Bidiyon ya ci gaba da yaɗuwa a kafafen sada zumunta, inda masu amfani da kafar X suka bayyana ra’ayoyinsu kan rabon kuɗin.

Wani mai amfani a kafar sada zumunta mai suna Fortunatus Ezuruike ya yi hasashen cewa kuɗin da ake rabawa na iya kasancewa daga cikin kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Mutanen Kano na cikin alheri, Gwamna Abba ya shirya rabon tallafin N50,000

Ya rubuta cewa:

“Na yi imanin wannan kuɗin tallafin man fetur ne. Gara a mayar da shi maimakon a bar waɗannan ’yan tsirarun su more rayuwa, yayin da ’yan Najeriya miliyan 200 ke shan wahala.”
Imaan.
Ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim da hoton yadda ta raba kudi a taron APC a Rivers Hoto: @hm_womenaffairs
Source: Twitter

Wani mai suna Crocmez ya kuma yi tambaya kan yadda gwamnati ke tafiyar da kuɗin da aka samu bayan cire tallafin, yana mai nuna damuwa kan ci gaba da karɓar bashi.

Ya rubuta cewa: “Ana dab da sake karɓar ƙarin bashi.”

Wata mai suna Mummy Lusty ta soki jam’iyyar APC mai mulki, inda ta yi hasashen cewa jam’iyyar za ta bar ƙasar cikin mummunan yanayi.

Ta rubuta cewa:

“APC za ta ƙarshe ta lalata wannan ƙasa. Zuwa lokacin da APC za ta gama da wannan ƙasa, babu abin da zai rage.”

Ra'ayoyin yan Najeriya kan tallafin N50,000

A wani labarin, kun ji cewa yan Najeriya na ci gaba da amfani da lambobin USSD domin tantance ko an zaɓe su cikin waɗanda za su cmsamu tallafin N50,000.

Wadanda suka samu tallafin sun nuna farin cikinsu tare da rokon gwamnati ta ci gaba da bullo da hanyoyin tallafawa talakawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262