Sule Lamido Ya Fadi Karyar da Shettima Ya Sharara a wajen Kamfen a Jigawa

Sule Lamido Ya Fadi Karyar da Shettima Ya Sharara a wajen Kamfen a Jigawa

  • Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya musanta ikirarin da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi na cewa yana goyon bayan jam'iyyar APC mai mulki
  • Lamido ya bayyana hakan ne a wani martani da ya yi, inda ya nuna mamakinsa kan yadda za a ce ya koma APC bayan bai goyi bayanta ba tun lokacin da aka kafa ta a 2014
  • Tsohon gwamnan ya yi amfani da kalmar Kanuri ta "kattuwunum" wacce ke nufin "ƙarya ce" don wulakanta kalaman na Shettima, tare da fitar da bayanin wani magoyin bayansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa – Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya fito fili ya yi watsi da ikirarin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, na cewa shi da wasu manyan ƴan siyasa a jihar na goyon bayan jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Jirgin ruwa ɗauke da kwamishina, jami'in NSCDC da wasu mutane ya yi hatsari

Sule Lamido ya nuna bacin ransa ne biyo bayan wani bidiyo ya nuna Shettima na cewa manyan mutanen jihar Jigawa, ciki har da tsohon gwamnan, suna tare da APC.

Sule Lamido a Jigawa
Tsohn gwamnan Jigawa, Sule Lamido. Hoto: Sule Lamido.
Source: Twitter

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa bidiyon ya fito da take cewa “Dukkan manyan mutanen jihar Jigawa suna tare da mu, ciki har da Sule Lamido.”

Sule Lamido ya karyata Shettima

Da yake mayar da martani a shafinsa na Facebook, Lamido ya yi mamakin yadda za a danganta shi da jam'iyyar ta APC, yana mai tunawa da cewa bai taɓa goyon bayanta ba tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2014.

Ya rubuta cewa:

“Ikon Allah. Ban yi APC a 2014 sai yanzu a 2026?”

Kazalika, Lamido ya ce duk da cewa kalaman sun fito ne daga bakin wani ɗan kabilar Kanuri, hakan bai ba shi mamaki ba, kafin daga bisani ya kammala da kalmar Kanuri ta “kattuwunum,” wacce ke nufin "ƙarya" ko "ba gaskiya ba."

Kashim Shettima a UN
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

An kare Sule Lamido

Bayan martanin nasa, tsohon gwamnan ya kuma wallafa bayanin wani magoyin bayansa mai suna Auwal Muhammed wanda ya yi tsayin daka wajen kare shi daga kalaman na Shettima.

Kara karanta wannan

Mustapha Kwankwaso zai dauki matakin sharia kan kwamishinan Abba, ya ba shi zabi

A cikin rubutun da magoyin bayan ya yi, ya bayyana cewa kalaman Shettima makirci ne na siyasa da nufin amfani da sunan Sule Lamido domin tallata wani samfurin siyasa da jama'a suka riga suka ƙi.

Sanarwar ta ƙara da cewa Sule Lamido na nan daram a jam'iyyar PDP kuma zai yi yaƙin neman zaɓe don ganin ta yi nasara daga sama har ƙasa a zaɓen 2027.

Shettima ya soki Obi

A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya zargi Peter Obi da lalata damar siyasarsa ta zaɓen 2027 ta hanyar yaɗa ƙarya da kuma amfani da alkaluma marasa tushe.

Shettima ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar NDC ya rasa farin jinin da yake da shi a baya kuma kalamansa ba su da wani tasiri mai kyau a wurin 'yan Najeriya a yanzu.

Mataimakin shugaban kasar ya yi waɗannan kalaman ne a wajen wani gangami na jam’iyyar APC da aka gudanar a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom a makon da ya wuce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng