Gwamna Ya Hango Abin da ba Zai Wa Yan Najeriya Dadi ba kan Dawo da Tallafin Fetur
- Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya ce tallafin man fetur da aka cire a Najeriya yana ƙarfafa almubazzaranci da cin hanci
- Otti ya goyi bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi, yana gargadin kada a mayar da shi
- Ya ce gwamnati ta fi dacewa ta karkatar da kuɗaɗenta wajen tallafa wa samar da kayayyaki da kasuwanci domin inganta rayuwar yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya soki tsarin tallafin mai, yana mai cewa tallafawa kayayyaki maimakon samar da su yana ƙarfafa rashin inganci da cin hanci da rashawa.
Gwamna Otti, wanda yake cikin jam’iyyar adawa ta LP, ya sake bayyana goyon bayansa ga wasu manufofin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

Source: Facebook
Gwamna Otti ya goyi bayan cire tallafi

Kara karanta wannan
"Allah ne ya cece ni," Gwamna ya ba da labarin yadda aka yi yunkurin kashe shi a gidansa
A wata hira da Arise TV ranar Alhamis, Otti ya goyi bayan matakin gwamnatin Tinubu na cire tallafin man fetur, tare da gargadin kada a yi ƙoƙarin mayar da tallafin.
Ya ce ya kamata gwamnati ta karkatar da kuɗaɗenta wajen tallafa wa samar da kayayyaki da kuma ƙirƙirar tsarin da zai ba ’yan kasuwa damar gudanar da harkokinsu yadda ya kamata.
“Na kasance mai tsayawa kan matsayina game da tallafi. Na kuma yi rubuce-rubuce da dama a kai,” in ji Otti.
Gwamna Otti ya kare cire tallafin
Gwamnan ya ƙara da cewa tallafa wa amfani da kayayyaki bayan sun kai matakin shiga kasuwa na iya ƙarfafa almubazzaranci tare da samar da damar yin amfani da tsarin ta hanyar da ba ta dace ba.
Ya ce mutanen da ke amfani da kayayyaki sukan fi kula da yadda suke amfani da su idan su ne ke ɗaukar kuɗinsu su saya da kansu.
Otti ya ce cire tallafin man fetur (PMS) tun farko shi ne matakin da ya dace, duk da wahalhalun da manufar ta jefa ’yan Najeriya ciki.
Gwamnan ya ce:
“Kun san yayin da zaɓe ke gabatowa, mutane za su riƙa gabatar da hujjoji iri-iri. Amma cire tallafin shi ne abin da ya dace a yi. Idan kana neman a dawo da tallafin mai, to ba ka yi wa ƙasar nan fatan alheri.”

Kara karanta wannan
Magana ta fito, an ji abin da ya faru da fitaccen jarumi fim a Najeriya kwanaki 5 kafin ya rasu

Source: Twitter
Ya nemi inganta wutar lantarki
Gwamna Otti ya ce ’yan kasuwa ba lallai ne su buƙaci tallafi ba idan gwamnati za ta iya tabbatar da samun wutar lantarki mai inganci a kai a kai, kamar yadda The Cable ta rahoto.
“Ga mutanen da ke amfani da lantarki wajen samar da kayayyaki da gudanar da masana’antunsu, a gaskiya ba sa buƙatar tallafin.
"Abin da suke buƙata kawai shi ne samun wutar lantarki a kai a kai. Da zarar ka iya tabbatar musu da wutar lantarki a kai a kai, za su biya,” in ji shi.
Gwamna Otti ya tsallake rijiya da baya
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya bayyana yadda ya tsira daga wani hari da ya kira yunƙurin kashe shi a 2015.
Ya ce a lokacin yana Abuja yana ƙoƙarin ganawa da wani mutum, amma mutumin ya ci gaba da sauya ranakun ganawar har ta kai ga ba a yi taron ba.
Asali: Legit.ng