Jerin Manufofin Shugaba Tinubu 4 da Wasu Gwamnoni Suka Yi Fito Na Fito da Su
Abuja - Tun daga hawansa mulki a watan Mayun 2023, shugaba Bola Tinubu ya aiwatar da manufofi da dama da wasu gwamnoni suka soki ko suka nuna rashin amincewa da su.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wasu gwamnonin sun nuna damuwa ne kan hanyar da shugaban kasa ya bi wajen aiwatar da manufofin ba tare da tuntuɓarsu ko tanadin abin da zai biyo baya ba.

Asali: Twitter
A baya-bayan nan gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya fito ƙarara ya soki tsare-tsaren tattalin arziki na Bola Ahmed Tinubu, rahoton AIT News.
A cewarsa, mutane na fama da yunwa da wahalhalu daban-daban sakamakon wasu manufofin da gwamnatin tarayya ta aiwatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika, a kwanakin baya gwamnan Bauchi, Bala Muhammed ya yi musayar yawu da fadar shugaban ƙasa kan tsare-tsaren tattalin arzikin Shugaba Tinubu, cewar jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan
"Shirin gwamnati ya gaza, " Tsohon gwamnan APC ya fito da matsalolin mulkin Tinubu
A wannan babin, Legit Hausa ta tattaro muku matakan da Tinubu ya ɗauka waɗanda gwamnoni suka fito suka soke su, ga su kamar haka:
1. Kudirin sauya fasalin haraji
Kudirin haraji na ɗaya daga cikin tsare-tsaren Bola Tinubu da ya fuskanci turjiya daga kusan gaba ɗaya gwamnonin Najeriya.
Rahoton Arise TV ya nuna cewa tun bayan gabatar da kudirorin dokar guda huɗu na sauya fasalin haraji a gaban Majalisa, gwamnonin Arewa 19 suka yi fatali da su gaba ɗaya.
A cewarsu, tanade-tanaden da ke cikin kudirorin za su yi wa Arewa illa babba, wasu daga cikin jihohin Arewa ba za su iya biyan albashi ba idan kudororin suka zama doka.
Haka zalika a wata hira da aka yi da shi a Channels tv, hadimin shugaban ƙasa, Daniel Bwala ya ce har gwamnonin Kudu ba su goyon bayan kudirin amma ba su fito sun yi magana ba.
Bwala ya ce wasu daga cikin gwamnonin Kudancin Najeriya sun nuna adawa da kudirin amma ba su fito bainar jama'a sun bayyana ba kamar yadda na Arewa suka yi.
A ƴan makonnin da suka wuce, ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta zauna ta sake nazari kan batun sauya fasalin harajin kuma ta amince da shi, rahoton Bussiness Day.
Sai dai gwamnonin jihohi 36 sun bukaci gwamnatin tarayya ta yi gyare-gyare a kudirin musamman dangane da abin da ya shafi rabon harajin kayayyaki watau VAT.
2. Ƴancin ƙananan hukumomi
Batun sakar wa kananan hukumomi mara su rika karɓar kasonsu kai tsaye daga asusun tarayya bai yi wa gwamnoni da dama daɗi ba.
Sai dai tun farko shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tunkari kotun ƙoli ne kai tsaye, wacce ta yanke hukuncin da ya ƴanta ƙananan hukumomin Najeriya.
Wannan ya sa ƴancin kananan hukumomi da tura masu kaso kai tsaye daga asusun tarayya ya zama doka bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Bayan wannan hukunci, gwamnoni suka fara shirye-shiryen gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi domin cika umarnin kotu mai daraja ta ɗaya a ƙasa.
Wasu gwamnonin sun nuna rashin gamsuwa da ƴancin ƙananan hukumomi, a ganinsu za a ƙara buɗe ƙofar cin hanci da rashawa idan hakan ta faru.
Misali, gwamnan Anambra, Charles Soludo ya soki matakin ƴancin ƙananan hukumomi, kuma ya kirkiro wata doka da kowace ƙaramar hukuma za ta rika ba da wani adadi na kasonta duk wata.
Sai dai da suka kai masa ziyara a Legas, Tinubu ya bai wa gwamnonin tabbacin cewa ba shi da shirin karɓe kananan hukumomi daga hanninsu kamar yadda ake yayatawa.
Hadimin shugaban kasa kan harkokin sadarwa na zamani, Dada Olusegun ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a shafinsa na X.
3. Cire tallafin man fetur
A ranar rantsar da shi, a watan Mayun 2023, shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a Najeriya.
Wannan mataki ya haddasa tashin farashin man fetur wanda lokaci guda ya kai kusan N600, lamarin da ya jawo fushin jama'a.

Kara karanta wannan
"A ajiye duk manufar da za ta wahalar da talaka," Gwamna ya soki tsare tsaren Tinubu
Wasu gwamnoni sun nuna damuwa kan yadda aka aiwatar da matakin ba tare da isasshen shiri ba ko hanyoyin rage radadin da zai biyo baya ga ‘yan kasa.
Alal misali, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya fito ya soki cire tallafin man fetur, yana mai cewa matakin bai zo a lokacin da ya dace ba, rahoton Vanguard.
Sai dai kamar yadda Gazettengr ta ruwaito, Makinde ya tabbatarwa mutanen Oyo cewa gwamnatinsa za ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen rage masu raɗaɗin cire tallafin.
3. Sauya tsarin kasuwar canjin kudi
A watan Yunin 2023, gwamnatin Tinubu ta canza tsarin musayar kudin waje domin barin Naira ta dogara da kanta ma'ana yanayin kasuwa zai yanke farashinta.
Wannan mataki ya haddasa karyewar darajar Naira da kuma hauhawar farashin kayayyyaki a faɗin ƙasar nan.
Wasu gwamnoni sun koka kan yadda hakan ke shafar tattalin arzikin jihohinsu, tare da zargin cewa ba a tuntube su ba kafin daukar matakin.
The Sun ta rahoto gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori na sukar tsare-tsaren tattalin arzikin Bola Tinubu wanda ya ƙunshi canza tsarin musayar kuɗi da cire tallafi.
Oborevwori ya danganta matsalar yunwa, fatara da rashin aikin yi da ‘yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu ga manufofin tattalin arziki na gwamnatin APC.
Sai dai duk da haka galibin gwamnonin da ke fitowa su soki tsare-tsaren gwamnatin tarayya, su kan dawo daga bisani su goyi bayan shugaban ƙasa.
Tinubu ya nemi a ƙara kasafin 2025
A wani labarin, kun ji cewa Bola Tinubu ya aika saƙo zuwa Majalisar dattawa, yana neman ta ƙara kuɗin da kasafin 2025 zai laƙume daga N49.7trn zuwa N54.2trn.
A cewar wasikar da Tiinubu ya tura Majalisar, karin ya biyo bayan samun N1.4trn daga hukumar FIRS da kuma N1.2trn daga Hukumar Kwastam.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng