Gombe: Ana Neman Hana Pantami Takara a PDP, za a Garzaya Kotu

Gombe: Ana Neman Hana Pantami Takara a PDP, za a Garzaya Kotu

  • Mai neman takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Gombe, Abdulkadir Hamma Saleh, ya yi watsi da tsayar da tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami
  • Da yake zantawa da ‘yan jarida a Gombe, Hamma Saleh ya ce ba a yi wa sauran masu neman takarar gwamna adalci ba wajen tsayar da Sheikh Pantami
  • Ya soki dage zaben fitar gwani da aka shirya gudanarwa ranar Lahadi zuwa ranar Talata, yana mai cewa ya yi mamakin jin cewa Pantami ya shiga neman takarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Daya daga cikin masu neman takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Gombe, Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, ya yi watsi da tsayar da Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin dan takarar gwamna.

Kara karanta wannan

Pantami ya fadi dalilin neman tikitin takarar gwamnan Gombe a PDP

Hakan na zuwa ne bayan Sheikh Pantami ya koma jam'iyyar PDP bayan ya janye daga zaben fitar da gwani da APC ta gudanar a Gombe.

Sheikh Isa Ali Pantami da Abdulkadir Hamma Saleh
Sheikh Isa Ali Pantami a hagu, a Abdulkadir Hamma Saleh a dama. Hoto: Abba Sani Pantami|Alh Sadeeq Gidado
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito yadda Pantami ya zama dan takarar gwamna na PDP ta hanyar amincewa da murya yayin zaben fitar da gwani na jam’iyyar da aka gudanar ranar Talata gabanin zaben gwamna na shekarar 2027.

Korafin mai neman takara a PDP

Da yake jawabi ga ‘yan jarida a gidansa da ke Gombe, Hamma Saleh ya bayyana tsayar da Pantami a matsayin rashin adalci ga sauran masu neman takara wadanda, a cewarsa, sun sayi fom din takara.

Ya ce an dage zaben fitar da gwani da aka shirya gudanarwa ranar Lahadi zuwa ranar Talata, yana mai cewa ya yi mamakin jin cewa Pantami ya zama dan takarar jam’iyyar.

“Yayin da muke jiran gudanar da zaben fitar da gwani ranar Lahadi, sai aka sanar mana kwatsam cewa an mayar da shi zuwa ranar Talata.
“Ba tare da wani bayani daga shugabannin jam’iyyar ba, sai muka wayi gari yau da labarin cewa Isa Pantami ya zama dan takarar gwamna na PDP,”

Kara karanta wannan

Pantami ya fice daga jam'iyyar APC, ya samu tikitin takarar gwamna a jihar Gombe

In ji shi.

Lokacin da PDP ta ba Pantami takara
Sheikh Isa Ali Pantami da jagororin PDP a Gombe. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Za a shigar da Pantami kotu

Hamma Saleh ya kuma nuna shakku kan yadda Pantami ya shiga zaben fitar da gwani na PDP, yana mai zargin cewa a baya ya shiga zaben fitar da gwani na APC da aka gudanar ranar 21 ga Mayu, 2026.

Ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben a kotu tare da bukatar magoya bayansa su kwantar da hankalinsu su ci gaba da bin doka yayin da lauyoyinsa ke bibiyar lamarin.

Daily Post ta rahoto ya ce:

“Ina Allah-wadai da abin da nake kallon rashin adalci ne a kaina da sauran masu neman takara. Lauyoyina sun fara aiki kan lamarin, kuma za mu nemi hakkimu ta hanyoyin shari’a da suka dace,”

Tinka zai yi takara a Gombe

A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar adawa ta ADC ta tsayar da Dr Bala Bello Tinka a matsayin dan takarar gwamna a jihar Gombe.

ADC ta zabi Dr Bala Bello ne bayan jam'iyyar APC ta fitar da Dr Jamilu Isiyaku Gwamna a matsayin wanda zai mata takarar gwamna a jihar.

Tinka dan kasuwa ne da ya shahara a jihar Gombe, kuma ya sha neman takara a matakai daban-daban a baya ba tare da samun tikiti ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng