‘Kokarin Matawalle a Harkar Tsaro Ya Sa Tinubu Ya Sanya Shi a Kamfen Dinsa’

‘Kokarin Matawalle a Harkar Tsaro Ya Sa Tinubu Ya Sanya Shi a Kamfen Dinsa’

  • Ma’aikatar Tsaro ta yaba da naɗin Bello Matawalle a cikin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu na 2027
  • Ma’aikatar ta ce naɗin ya nuna amincewar Tinubu da ƙwarewar Matawalle wajen gudanar da harkokin gwamnati
  • Matawalle ya gode wa Tinubu da shugabannin APC, tare da yin alƙawarin amfani da ƙwarewarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ma’aikatar Tsaro ta yaba da naɗin Ministan Ƙasa na Tsaro, Bello Matawalle, a matsayin Mataimakin Daraktan Tsaro da Leken Asiri na ɗaya.

Matawalle zai riƙe wannan matsayi ne a Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC na shekarar 2027.

An yaba wa Tinubu kan mutunta Matawalle a kwamitin kwamfe
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da Babbar Jami’ar Yaɗa Labarai, Queeneth Iheoma-Hart, ta fitar ranar Lahadi a Facebook.

'Abin da ya sa Tinubu ya dauki Matawalle'

Ta ce ƙwarewar tsohon gwamnan Zamfara ta haɗa da aikin gwamnati, gudanar da harkokin tsaro da kuma tattara goyon bayan siyasa.

Kara karanta wannan

Maganar Wike ka iya son tabbata, gefen Atiku,Obi sun magantu kan yiwuwar hadaka

Ma’aikatar ta ce a matsayinsa na Mataimakin Daraktan Tsaro da Leken Asiri na ɗaya, Matawalle zai kula da tsarin tsaron ayyukan kamfen a faɗin ƙasar.

Hakan zai haɗa da tabbatar da tsaron ’yan takara, jami’an kamfen da magoya bayansu a duk faɗin Najeriya.

Haka kuma, zai kasance mai kula da leken asiri da tantance haɗarin tsaro, tare da haɗa kai da hukumomin tsaro wajen gano barazana da rage haɗarinta.

Ma’aikatar ta ce Matawalle zai kuma jagoranci haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki wajen gudanar da ayyukan kamfen.

Za a samu hakan ne ta hanyar hulɗa da sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma, ƙungiyoyin matasa da mata domin ƙarfafa tsarin tsaro na kamfen.

Ma’aikatar ta ƙara da cewa naɗin tsohon gwamnan Zamfara ya nuna amincewar Tinubu da tarihin Matawalle wajen gudanar da ayyukan gwamnati, tsaro da tattara goyon bayan siyasa.

Ta kuma bayyana cewa a matsayinsa na Ministan Ƙasa na Tsaro, Matawalle ya taimaka wajen aiwatar da manufofin gwamnatin Tinubu kan tsaro.

Ta ce ya yi hakan ta hanyar aiwatar da manufofi, hulɗa da hukumomin tsaro da kuma tallafa wa jin daɗin sojoji da inganta kayayyakin aikinsu.

Kara karanta wannan

Sanatan da ya fice daga APC ya samu tikitin PDP, zai fafata da gwamna a 2027

Da yake mayar da martani kan naɗin, Matawalle ya gode wa Tinubu da shugabannin APC saboda amincewar da suka nuna masa.

Ya yi alƙawarin amfani da ƙwarewar da ya samu a matsayinsa na tsohon gwamna, Ministan Tarayyar Najeriya kuma gogaggen jagoran siyasa.

Matawalle ya ce zai yi amfani da wannan ƙwarewa wajen tabbatar da kamfen mai zaman lafiya, tsari da nasara a faɗin Najeriya.

An saka Betta Edu a kamfen Tinubu

A wani labarin, an ji cewa an saka tsohuwar ministar jin ƙai Betta Edu da wasu da ake zargi da badakala a Najeriya cikin kwamitin yaƙin neman zaben APC na 2027.

Betta Edu za ta kasance daraktar wayar da kan mata, Ngozi Olejeme za ta jagoranci shirye-shiryen zaɓe da haɗa kai a Kudu maso Kudu.

Edu ta fuskanci binciken EFCC, yayin da Olejeme ke fuskantar shari’ar zargin karkatar da Naira biliyan 1.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.