Zaben 2023: Wike Ya Bayyana Abin da Ya Yi Shirin Yi da Atiku Ya Kayar da Tinubu

Zaben 2023: Wike Ya Bayyana Abin da Ya Yi Shirin Yi da Atiku Ya Kayar da Tinubu

  • Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa ya shirya ficewa daga Najeriya kafin Kotun Ƙoli ta yanke hukunci kan zaɓen shugaban ƙasa na 2023
  • Wike yace ya yanke shawarar barin Najeriya idan Atiku Abubakar ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023
  • Tsohon gwamnan na Ribas ya bayyana cewa ya samu labarin makirce-makircen da aka shirya masa saboda goyon bayan da yake ba Bola Tinubu a lokacin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana shirin da ya yi da a ce Shugaba Bola Tinubu ya faɗi zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Nyesom Wike ya bayyana cewa ya so ya tattara ƴan komatsansa ya fice daga ƙasar nan da Tinubu bai yi nasara ba a zaɓen.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ɗauki zafi kan rikicinsa da ministan Tinubu, ya faɗi dalilin amincewa da sulhu

Wike ya yi magana kan zaben 2023
Wike ya so ficewa Najeriya da Atiku ya ci zaben 2023 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nyesom Wike - CON, GSSRS, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A wata hira da aka yi da shi kai tsaye a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu, Wike ya bayyana cewa ya shirya ficewa daga Najeriya da Atiku Abubakar ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Wike ya yi shirin yi?

Ministan na babban birnin tarayya Abuja, ya bayyana cewa ya riga ya shirya fasfo ɗinsa kafin yanke hukuncin Kotun Ƙoli, domin barin ƙasar nan idan kotun ta ba Atiku Abubakar nasara.

Ya ƙara da cewa an sanar da shi maƙarƙashiyar da aka ƙulla masa saboda nuna adawa da takarar Atiku a zaɓen shugaban ƙasan, kamar yadda gidan talabijin na Arise ya ruwaito.

A kalamansa:

"Lokacin da muka je Kotun Ƙoli, na sanya fasfo ɗina a cikin jakata.
"Kuma na gayawa matata, idan muka yi rashin nasara a yau, daga nan zan wuce. Saboda haka ki kula da wannan, ki kula da wancan. Dukkanin waɗannan mutanen, na san gaba ɗaya shirin da suka ƙulla a kaina.

Kara karanta wannan

Daga karshe Wike ya bayyana inda aka kwana kan rikicinsa da Gwamna Fubara

Jaridar PM News ta ce a yayin ganawa da manema labaran Wike ya bayyana cewa yanzu ba ya inuwa ɗaya tare da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara.

Wike ya bada tallafi ga musulmai

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ba al’ummar Musulmai a birnin Abuja da kayan abinci.

Ministan ya yi wannan kyautar ne domin taimakawa Musulmai da suke azumin watan Ramadan a birnin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel