Matsala Ta Kunno a APC Tun kafin Zaben 2027, Wani Tsagi na Neman Tikiti a 2031

Matsala Ta Kunno a APC Tun kafin Zaben 2027, Wani Tsagi na Neman Tikiti a 2031

  • Tsofaffin mambobin ANPP sun nemi APC ta ba tsohon ɓangaren jam’iyyar tikitin takarar shugaban ƙasa a zaben 2031
  • Sun ce CPC ta samar da Muhammadu Buhari, yayin da Bola Tinubu ya fito daga ACN, don haka lokaci ya yi na ANPP
  • Tsofaffin mambobin sun kuma nemi Tinubu ya ƙara musu mukamai, tare da barin kujerar mataimakin shugaban ƙasa a hannun ɓangarensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsofaffin mambobin jam’iyyar ANPP da aka yi hadaka aka kafa APC sun tayar da rigima kan zaben 2031.

Mambobin sun nemi a ba ɓangarensu tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a shekarar 2031.

Rikici na neman tashi a APC kan zaben 2031
Marigayi Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Malam Garba Shehu, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

An bayyana wannan matsaya ne cikin wata sanarwa da tsoffin mambobin ANPP suka fitar ranar Litinin, 7 ga Satumba, 2026, bayan taronsu a Abuja, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tinubu bai cire kansa ba, ya faɗi irin shugabannin da Najeriya ke buƙata

Abin da tsofaffin mambobin ANPP ke bukata

Tsofaffin mambobin ANPP sun ce buƙatarsu ta samo asali ne daga bukatar tabbatar da adalci da daidaito tsakanin tsoffin ɓangarorin siyasa da suka kafa APC.

Sun bayyana cewa ɓangaren Congress for Progressive Change, CPC, ya samar da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya yi wa’adin mulki biyu.

A halin yanzu kuma, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya fito daga tsohon ɓangaren ACN, ne ke jagorantar ƙasar, in ji tsoffin mambobin ANPP.

Sun ce tun da sun taimaka wajen kafa APC kuma suka ci gaba da kasancewa cikin tsarin siyasar jam’iyyar, ya kamata a yi la’akari da ɓangaren ANPP wajen samar da shugaban ƙasa.

A cewarsu, hakan ya kamata ya faru ne bayan wa’adin mulkin Shugaba Bola Tinubu ya kare a shekarar 2031, domin tabbatar da daidaito tsakanin ɓangarorin da suka kafa APC.

Sun kuma yi kira ga Shugaba Tinubu da ya ƙara wakilcin tsoffin mambobin ANPP a gwamnatinsa, ta hanyar ba su muhimman mukamai a hukumomin gwamnati.

Kara karanta wannan

Sanata Hanga, Gaya da mutane fiye da 100,000 sun tattara komatsansu zuwa APC

Tsofaffin mambobin ANPP na neman a ba su dama a 2031
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin taro a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Sun bukaci kujerar mataimakin shugaban kasa

Haka kuma, tsofaffin mambobin sun dage cewa kujerar mataimakin shugaban ƙasa ya kamata ta ci gaba da kasancewa a hannun ɓangaren ANPP.

Sun bayyana ANPP a matsayin ɓangare na biyu mafi girman gudummawa wajen kafa APC, tare da nuna godiya ga Tinubu kan abin da suka ce ya zama kyakkyawar amsa ga wasu buƙatunsu.

Sun ce waɗannan buƙatu sun fito ne daga taron da suka gudanar ranar 3 ga Nuwamba, 2025, inda suka gabatar da wasu buƙatu ga Shugaba Tinubu.

Yayin da suke yabawa Shugaban Ƙasa kan ci gaba da riƙe Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, sun bayyana wasu naɗe-naɗe a matsayin alamar amincewa da ɓangarensu.

Sun ambaci naɗin Sanata Abdulaziz Abubakar Yari a matsayin Darakta-Janar na Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu ta 2027 a matsayin ɗaya daga cikin misalan hakan, cewar Leadership.

Tinubu ya tuna alherin marigayi Buhari

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027 ta fara zafi, Obi da Kwankwaso sun tura ƙalubale ga ƴan Najeriya

A baya, an ji cewa shugaba Bola Tinubu ya bayyana marigayi Muhammadu Buhari a matsayin abin koyi saboda gaskiya, rikon amana da kaunar 'yan kasa.

Tinubu ya ce abin koyi da Buhari ya bari ba mukamai ko ayarin motoci ba ne, illa gaskiya, saukin kai da daukar mulki a matsayin amanar jama’a.

Shugaban ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba da aikin da Buhari ya fara domin mutunta tarihinsa da kuma gina kasa mai adalci a nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.