'Yan Ɗariƙa a Katsina Sun Tsaida wa Mabiya waɗanda za su zaɓa a 2027
- ‘Yan ɗariƙa za su zabi shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamna Dikko Umaru Radda a Katsina a takarar 2027
- Ma’assasa Sheikh Ɗahiru Bauchi ta nuna goyon bayanta ga ‘yan takaran jam’iyyar APC a wajen wani taro
- Sheikh Nasiru Ɗahiru Bauchi ya bayyana wannan da ya halarci rabon kaya da Abdul’aziz Maituraka ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Katsina - Mai girma Diko Umaru Radda ya samu kwarin guiwar takarar gwamna da yake sake yi a jihar Katsina a zaben 2027.
Gwamnan ya samu goyon bayan wasu kungiyoyin ɗariƙa wadanda suke ganin dacewar ya zarce a kan kujerarsa har zuwa 2031.

Source: Facebook
‘Yan ɗariƙar sun shaida wa duniya goyon bayan su wajen wani taro da aka shirya domin tallafa wa jama’a in ji hadimin gwamnan.
Mustapha Sama’ila Ingawa ya fitar da bayanin dalla-dalla a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.
Abdul’aziz Maituraka ya tallafa wa mata a Katsina
Gwamna Dikko Radda ya samu halartar taron raba tallafin sana’a ga mata 500 da Abdul’aziz Maituraka ya shirya a garin Katsina.
Alhaji Abdul’aziz Maituraka ya raba wa mata 500 kyautar N10, 000 da kuma wanke da man gyara domin bunkasa kasuwancinsu.
Hadimin tsohon gwamnan ya yi wannan ne da nufin rage raɗaɗi da ake ciki da kuma ganin waɗannan mata sun iya dogara da kansu.
Maituraka wanda ya yi aiki da gwamnatin Aminu Bello Masari ya saba irin wannan kyauta a Katsina ta karkashin gidauniyarsa.
Jagororin darika sun gamsu da Tinubu da Radda
A jawabin da ya yi a ɗakin taro na Ameera Event, wakilin ma’assasa Sheikh Ɗahiru Bauchi, ya gode wa gwamnatin Dikko Radda.
Sheikh Nasiru Ɗahiru Bauchi ya ce Mai girma Radda ya bi tafarkin Aminu Bello Masari wajen dama wa da mabiya ɗariƙa a mulkinsa.
A nan ne ya bayyana cewa suna tare da gwamnatin Dikko da kuma Bola Ahmed Tinubu mai neman zarcewa a kujerar shugaban kasa.
Tsohon gwamna da shugabannin jam'iyya sun tallata APC
Jawabin ya ce Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya ji dadin yadda aka taimaka matan, ya yabi aikin da tsohon mai ba shi shawaran ya yi.
Tsohon gwamnan kuma jagora a APC ya yi amfani da damar wajen tallata Bola Tinubu a Katsina.
Alhaji Bala Abu Musawa wanda shi ne Mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC a jihar Katsina, ya yi magana a wajen taron rabon kaya.
Bala Abu Musawa ya bukaci a dage da fadakar da jama’a game da irin alheran da Dikko Radda da Bola Tinubu suka kawo a jihar.
Jawabin Dikko Radda a wajen taron rabon tallafin
Shi ma Mai girma Malam Dikko Umaru Radda, ya jinjina wa tallafin kayan sana’an da Abdul’aziz Maituraka ya raba wa mata.
Radda ya yi kira ga jama’a su cigaba da ba Bola Tinubu goyon baya, ya ce wannan zai sa su ga alheran gwamnatin tarayya.
Gwamnan Katsina bai bar wurin ba sai da ya caccaki ‘yan adawa da ke takarar 2027, ya ce wasunsun suna yaudarar jama’a ne.
Tsohon sanata ya ce Arewa ta kyale Tinubu
Shehu Sani ya ce a 2027 ya kamata Bola Tinubu, Peter Obi da sauran ‘yan Kudu su fafata ne a tsakaninsu, Arewa ta jira sai a shekarar 2031.
Kwamred ya ce bai dace wani ɗan takara daga Arewa kamar Atiku Abubakar ya nemi mulki ba, ya kamata a bar Kudu ta kammala wa'adinta biyu.
A maimakon haka, ya buƙaci 'yan takara daga Kudu kamar Peter Obi, Omoyele Sowore, Seyi Makinde da Donald Duke su fafata da APC.
Asali: Legit.ng


