Yanzu Yanzu: Wani babban jigon APC ya sauya sheka zuwa PDP a Rivers (hotuna)

Yanzu Yanzu: Wani babban jigon APC ya sauya sheka zuwa PDP a Rivers (hotuna)

- Jam’iyyar APC a jihar Rivers ta rasa daya daga cikin manyan jiga-jiganta, Ambrose Nwuzi zuwa PDP

- Nwuzi da magoya bayansa sun sauya sheka zuwa PDP a karamar hukumar Etche a ranar Lahadi, 30 ga watan Agusta

- Gwamna Wike ne ya tarbi sabbin mambobin tare da basu tabbacin samun kula iri guda

Wani babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Rivers, Cif Ambrose Nwuzi, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

A wani dan kwarya-kwaryan biki da aka yi a garin Afara a karamar hukumar Etche a ranar Lahadi, 30 ga watan Agusta, Gwamna Nyesom Wike ya tarbi tsohon Shugaban na AP da magoya bayansa zuwa PDP, a bisa rahoto daga Rivers News Today.

Ya yake yi wa tsohon Shugaban na APC maraba da zuwa PDP, Gwamna Wike ya yi bayanin cewa sabbi da tsoffin mambobin duk za su samu kula iri guda a jam’iyyar.

Yanzu Yanzu: Wani babban jigon APC ya sauya sheka zuwa PDP a Rivers (hotuna)
Yanzu Yanzu: Wani babban jigon APC ya sauya sheka zuwa PDP a Rivers Hoto: Rivers Todays News
Asali: Facebook

Ya kuma bukaci Shugaban PDP a karamar hukumar Etche, Prince Emma Anyanwu, da ya hada kan jam’iyyar da kuma tabbatar da gudunmawar dukkanin masu ruwa da tsaki.

KU KARANTA KUMA: Zamfara za ta fara yankewa masu tukin ganganci hukuncin kisa bayan mutuwar wasu magoya bayan gwamnan su 15

Da yake magana a taron, Cif Nwuzi ya yi godiya ga gwamnan jihar Rivers da PDP a kan tarbansa da suka yi tare da magoya bayansa.

Ya yi alkawarin tabbatar da ganin ya dawo da abokansa da ke APC zuwa PDP nan da dan lokaci.

A wani labari na daban, mun ji cewa gabannin zabukan gwamnoni a jihohin Edo da Ondo, rundunar ‘yan sanda ta bayyana yiwuwar barkewar rikici, hare-hare daga abokan adawa, da kuma watsa bayanan karya a matsayin babban barazanar tsaro ga zabukan.

An shirya gudanar da zabuka a Edo da Ondo a ranar 19 ga watan Satumba da 10 ga watan Oktoba.

Sufeto janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu ya gargadi ‘yan siyasa da magoya bayansu da su kama kansu sosai ta hanyar bin doka.

Ya kuma shawarce su da su guji duk wani abu da ka iya kawo matsala a gudanarwar zabe a jihohin biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel