Gwamnonin APC Sun Yi Taro, Sun Bayyana Sabuwar Matsayarsu kan 2027
- Gwamnonin jam'iyyar APC sun bayyana cewa ba za su goyi bayan wani ƙawance ko haɗaka da wasu jam'iyyu ba a zaɓen 2027
- Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Hope Uzodinma, ya bayyana cewa irin wannan tsari zai haifar da rikice-rikice ga 'yan takarar jam'iyyar
- Gwamnonin sun jaddada cewa goyon bayansu yana nan ga Shugaba Bola Tinubu da sauran 'yan takarar APC kawai a kowane mataki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC sun barranta da duk wani nau'in ƙawance na siyasa gabanin zaɓen shekara ta 2027, inda suka ƙuduri aniyar goyon bayan 'yan takarar da jam'iyyar ta tsayar kawai.
A wani taro da suka gudanar a daren Litinin a masaukin gwamnan jihar Imo da ke Asokoro, Abuja, gwamnonin sun bayyana cewa irin waɗannan haɗaka ko ƙawance na iya barazana ga damar da 'yan takarar APC ke da ita.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Daliban manyan makarantun Arewa sun yi matsaya kan goyon bayan Tinubu

Source: Twitter
Jaridar Tribune ta ruwaito cewa wasu daga cikin tsofaffin jiga-jigan APC da suka rasa tikitin takara a zaɓen fitar da gwani sun koma jam'iyyar PDP inda suka sami tikitin takara.
2027: Matsayar gwamnonin APC
Da yake karanta matsaya da ƙungiyar ta ɗauka, Gwamnan jihar Imo kuma shugaban ƙungiyar, Sanata Hope Uzodinma, ya bayyana cewa gwamnonin sun amince gaba ɗaya cewa ba su da alaƙa da wani ƙawance.
Ya jaddada cewa irin wannan tsarin siyasa zai haifar da daure kai da kuma shafar nasarar zaɓen APC.
Ya rubuta cewa:
"Ƙungiyar ta amince gaba ɗaya cewa mambobinta ba za su shiga, goyon baya ko amincewa da wani ƙawance ko tsarin siyasa da ka iya raunana zaɓen sake neman takarar Shugaban Ƙasa, raunana APC ko shafar wani ɗan takarar jam'iyyar a kowane mataki ba.
"Muna da buƙatar haɗa dukkan ginin yaƙin neman zaɓenmu domin bin tsarin Shugaban Ƙasa da manufofin APC."
Tsayuwa a kan 'yan takarar APC
Gwamnonin sun tabbatar da cewa alƙawarin da suka ɗauka na goyon baya ya tsaya ne kawai ga 'yan takara da APC ta tsayar domin su ne jam'iyyar ke ɗaukar nauyinsu.
Punch ta wallafa cewa Uzodinma ya ƙara da cewa duk wani tsari da zai haifar da rarrabuwar kawunan magoya baya ko hamayya a cikin gida ba za a amince da shi ba gaba ɗaya.
Gwamnonin sun buƙaci dukkan ma'aikata da masu ruwa da tsaki a yaƙin neman zaɓen jam'iyyar da su bi umarnin da aka gindaya domin samun nasara a dukkan matakai.

Source: Facebook
Batun hadakar Obi da Makinde
A wani labarin daban, kun ji cewa sabuwar mu'amala tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, da Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, tana haifar da maganganu game da yiwuwar ƙulla ƙawancen jam'iyyun adawa.
Shugabannin guda biyu, waɗanda ke ɓangarori daban-daban a zaɓen shekarar 2023, an gan su tare a wani taro na sirri a Ibadan, sannan kuma suka bayyana tare wajen ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APM.
Majiyoyi daga ɓangarorin biyu sun bayyana cewa tattaunawarsu ta fi maida hankali ne kan "bukatun ƙasa, shugabanci, da kuma tsare-tsaren zaɓen 2027".
Asali: Legit.ng
