Asiri Ya Tonu: Yadda Iran Ta Lalata Jiragen Yakin Amurka Kusan 100

Asiri Ya Tonu: Yadda Iran Ta Lalata Jiragen Yakin Amurka Kusan 100

  • Wani rahoton Majalisar Dokokin Amurka ya ce akalla jiragen sojin Amurka 81 ne aka lalata ko suka samu matsala tun bayan fara yaƙin da Iran
  • Asarar ta haɗa da jiragen yaƙi, jirage marasa matuƙa da jirage masu saukar ungulu, inda kiyasin kuɗin maye gurbinsu ya kai dala biliyan 3.3
  • Rahoton ya kuma bayyana cewa jiragen MQ-9 Reaper guda 45 sun ɓace, lamarin da ya rage adadin jiragen irin wannan da Amurka ke da su zuwa 135

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington – Akalla jiragen sojin Amurka 81 ne aka rasa ko suka lalace tun bayan da Amurka ta fara hare-haren soji kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.

Rahoton cibiyar bincike ta CRS da aka sabunta ranar 5 ga Oktoban 2026 ya ce jiragen da abin ya shafa sun haɗa da jiragen yaƙi, jiragen leƙen asiri, jirage marasa matuƙa da jirage masu saukar ungulu.

Kara karanta wannan

Ana jimamin hatsarin sojoji, fasinja ya mutu a jirgin da ke kan hanyar zuwa Legas

Jirgin Amurka da Donald Trump
Jirgin Amurka a hagu, shugaba Donald Trump a dama. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

F-15E na cikin jiragen da aka rasa

New York Post ta wallafa cewa daga cikin jiragen da suka lalace ko aka rasa akwai F-15E Strike Eagle guda 12 da F-35A Lightning II guda ɗaya.

Rahoton ya ce wasu daga cikin F-15E sun faɗa ne sakamakon harbin sojojin Amurka da kansu a Kuwait, yayin da wasu suka lalace sakamakon hare-haren Iran.

Jiragen F-15E guda takwas da suka samu ƙananan matsaloli a wani harin Iran kan sansanin sojin Amurka da ke Jordan an gyara su kuma sun koma aiki.

An rasa MQ-9 guda 45

NDTV ta wallafa cewa wani babban kaso na asarar ya shafi jiragen MQ-9 Reaper marasa matuƙa, inda akalla 45 daga cikinsu suka ɓace.

Ana amfani da MQ-9 wajen leƙen asiri da kai hare-haren makami mai linzami, kuma ƙimar kowane jirgi tana tsakanin dala miliyan 30 zuwa 50.

Rahoton ya ce adadin Reaper da ke cikin rundunar ya ragu zuwa 135, yayin da Rundunar Sojin Sama ta Amurka ke da bukatar akalla 189 da za su kasance a shirye don tura su aiki.

Kara karanta wannan

Amurka da Saudiyya sun turo muhimmin saƙo zuwa Najeriya kan hatsarin jirgin sojojin sama

Sauran jiragen da Iran ta lalata

Rahoton ya kuma lissafa jiragen A-10 Thunderbolt II guda biyu, KC-135 Stratotanker guda bakwai da E-3 Sentry guda ɗaya cikin jiragen da suka rasa ko suka samu matsala.

Haka kuma akwai MC-130J Commando II guda biyu, HH-60W Jolly Green II guda ɗaya, MQ-4C Triton guda ɗaya da MQ-1 guda uku.

Sansanin sojin Amurka
Wani sansanin sojin Amurka da Iran ta kai wa hari. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Sauran sun haɗa da AH-64 Apache guda ɗaya, AH-6 Little Bird guda huɗu da MH-60 Sea Hawk guda ɗaya.

Sai dai CRS ta yi gargadin cewa adadin 81 na iya sauyawa, domin wasu bayanai na iya kasancewa ba a bayyana su ba, yayin da wasu jiragen da suka lalace suka koma aiki.

Rahoton ya ce kiyasin kuɗin da Amurka ta kashe kan yaƙin ya kai dala biliyan 43.6, bayan ya ƙaru da kusan dala biliyan 5 daga watan Agusta.

Za a kashe tsohon sojan Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Amurka ta amince da aiwatar da hukuncin kisa kan Nidal Hasan, tsohon babban soja a rundunar Amurka, ta hanyar harbin bindiga.

Kara karanta wannan

Lokuta 10 da aka samu jirgin sojoji ya yi hadari a Najeriya daga 2021 har 2026

Hasan ya kashe mutane 13 tare da raunata wasu 32 a wani harin da ya kai sansanin Fort Hood da ke Texas a shekarar 2009. An yanke masa hukuncin kisa a shekarar 2013 bayan wata kotun soji ta same shi da laifi.

An tsara aiwatar da hukuncin a ranar 3 ga Disamba, 2026, a Fort Hood, abin da zai zama karon farko da aka aiwatar da hukuncin kisa kan wani soja na Amurka tun shekarar 1961.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng