Babbar Nasara: An Ceto Matasa Yan NYSC da Yan Bindiga Suka Sace a Najeriya

Babbar Nasara: An Ceto Matasa Yan NYSC da Yan Bindiga Suka Sace a Najeriya

  • Jami'an tsaron hadin gwiwa sun samu nasarar ceto matasa 20 da ke shirin shiga aikin bautar kasa, NYSC da wani farar hula bayan an sace su a jihar Imo
  • Rundunar sojoji, jami'an hukumar DSS, ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro ne suka gudanar da aikin ceton
  • Rahotanni sun bayyana cewa yanzu an kai waɗanda aka ceto wani wuri mallakin hukumar DSS domin ba su kulawar lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Imo, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa dakarun tsaron Najeriya na hadin gwiwa sun yi nasarar ceto matasa 20 yan bautar kasa watau NYSC daga hannun masu garkuwa da mutane a Imo.

Jami'an tsaron sun ceto matasan ne bayan wasu miyagun yan bindiga sun yi garkuwa da su a hanyasu ta zuwa sansanin daukar horo na NYSC domin fara aikin yi wa kasa hidima.

Kara karanta wannan

An saki hoton gurgu da bingigogi da ke taimakon 'yan bindiga

Matasa.
Matasa masu yi wa kasa hidima yayin da suke tsakiyar daukar horo a sansanin NYSC Hoto: @NYSCNg
Source: Twitter

Jami'an tsaro sun ceto yan NYSC 20

Jaridar Vanguard ta ruwwito cewa an ceto mutum 20 da ke shirin shiga aikin yi wa ƙasa hidima na NYSC tare da wani farar hula nutum da aka sace a jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Bayanai sun tabbatar da cewa an cimma wannan nasara ne bayan wani samame da jami’an tsaro suka gudanar bisa sahihan bayanan sirri.

Dakarun Rundunar soji, Jami'sn Hukumar Tsaro Farin Kaya ta Ƙasa (DSS), ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro ne suka haɗa kai wajen gudanar da aikin ceton.

An ruwaito cewa an sace mutanen ne yayin da suke tafiya za su wuce ta jihar Imo, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka ƙaddamar da wani samame domin gano inda suke da kuma ceto su.

An kai waɗanda aka ceto ofishin DSS

A cewar majiyoyin tsaro, a halin yanzu ana duba lafiyar waɗanda aka ceto a wani wuri da yake mallakin hukumar DSS, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dan siyasa a Kano ya kira ruwa bayan nuna bindiga a wurin taro

Majiyoyin sun ce ana ci gaba da ƙoƙarin gano cikakkun bayanan yadda aka yi garkuwa da mutanen tare da kama sauran waɗanda ake zargin suna da hannu a lamarin.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262