Donald Duke: Dan Takara Ya Gama Shiri, Ya Fadi Yadda Zai Dawo da Fetur zuwa N300
- Tsohon gwamnan Cross River, Donald Duke, ya ce zai rage farashin fetur zuwa kusan N300 kan kowace lita idan ya zama shugaban Najeriya
- Duke ya ce ya kamata a ƙayyade farashin man da ake amfani da shi a cikin Najeriya ba bisa farashin kasuwar duniya ba
- Ɗan takarar PRP ya ce za a ware wani kaso na ɗanyen man Najeriya domin amfanin cikin gida, yayin da za a sayar da sauran man zuwa ƙasashen waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Gwamnan Jihar Cross River kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) a zaɓen 2027, Donald Duke, ya yi maganar rage farashin man fetur.
Donald Duke ya ce zai rage farashin fetur zuwa kusan N300 kan kowace lita idan aka zaɓe shi.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta fara bayani kan kudin cire tallafin fetur, ta fadi yadda ta kashe $500m

Source: Facebook
Duke ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar Channels Tv ranar Laraba, 7 ga watan Oktoban 2026.
Me Duke ya ce kan farashin fetur?
Tsohon gwamnan ya ce man fetur da ake samarwa domin amfanin cikin gida bai kamata a ƙididdige farashinsa bisa farashin kasuwar man fetur ta duniya ba.
A cewarsa, ya kamata a yi la’akari da kuɗin da ake kashewa wajen samar da man kafin a ƙayyade farashin da za a sayar wa ’yan Najeriya.
Duke ya soki tsarin tallafin man fetur, inda ya bayyana shi a matsayin abin da yake ganin bai dace ba.
“Zan sanya farashin man fetur da ake amfani da shi a cikin gida bisa kuɗin samarwa, ba bisa farashin kasuwar duniya ba.” In ji shi.
Ya ce zai rage fetur zuwa N300
Da aka tambaye shi farashin da yake ganin zai iya yiwuwa a ƙarƙashin mulkinsa, Duke ya ce zai yi ƙoƙarin rage shi zuwa kusan N300 kan kowace lita.
Ya ce ko da yake mutane na iya ganin wannan farashin ba zai yiwu ba, ya yi imanin cewa lissafin da ya yi kan kuɗin samar da man yana ba da damar cimma hakan.
Duke ya kuma bayyana cewa tsadar fetur na ƙara wa ’yan Najeriya, musamman masu ƙaramin ƙarfi, nauyin wahalar rayuwa.
Ya yi nuni da cewa mafi ƙarancin albashi na N70,000 na iya ƙarewa wajen sayen fetur kawai, musamman ga masu amfani da motoci wajen ayyukan yau da kullum.
Shirin Duke kan ɗanyen man Najeriya
Duke ya ce shirin nasa zai ƙunshi ware wani kaso na ɗanyen man Najeriya domin amfanin cikin gida, yayin da za a sayar da sauran man a kasuwannin duniya.
Ya bayar da misalin ware ganga 600,000 na ɗanyen mai a kowace rana domin biyan bukatun cikin gida, idan wannan shi ne adadin da ake amfani da shi a kullum.
A cewarsa, za a iya sayar da sauran ganga kusan miliyan ɗaya a kasuwannin duniya domin samar da kuɗaɗen shiga.
Duke ya ce wannan tsari ne zai ba da damar rage farashin man da ake amfani da shi a Najeriya, yayin da ƙasar ke ci gaba da samun kuɗaɗen shiga daga sayar da ɗanyen mai zuwa ƙasashen waje.

Kara karanta wannan
An fara murna da gwamnatin Tinubu ta cika alkawarin da ta daukarwa sojojin Najeriya

Source: Facebook
Dalilin Donald Duke na fitowa takara
A wani labarin kuma, kun ji cewa Donald Duke, ya ce ya fito takara ne domin magance matsalolin da ke addabar Najeriya tare da bai wa 'yan kasar sabuwar damar rayuwa.
Duke ya nuna damuwarsa cewa Najeriya ta kasa shawo kan matsalar rashin ingantaccen shugabanci tun bayan komawa mulkin dimokuradiyya.
Asali: Legit.ng
