'Gari Ya Yi Zafi,' Tsohon Sanata Ya Fadi Halin da Ake ciki bayan Barin Majalisa
- Tsohon Sanata, Bala Ibn Na’Allah, ya bayyana cewa yawancin tsofaffin ‘yan majalisa ba sa iya biyan kudin makarantar ‘ya’yansu bayan barin ofis
- Ya ce ba wai yana fadin hakan ba ne don kare tsofaffin shugabanni ba, sai dai yana bayani ne kan gaskiyar abin da ke faruwa idan sun gama aiki
- A cikin karin bayani da ya yi, tsohon Sanatan wanda ya wakilci Kebbi ta Kudu a majalisa ta takwas, ya bayyana cewa tsofaffin ‘yan majalisa na jin jiki
- Ya ce wasu daga cikin masu rike da madafun iko kan shiga siyasa da zaton za su tara makudan kudi, amma daga baya su bar mukamansu a cikin matsi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon Sanata, Bala Ibn Na’Allah ya bayyana irin kalubalen da wasu ‘yan majalisar Najeriya ke fuskanta bayan sun bar kujerunsu.
Ya bayyana cewa da dama daga cikinsu ba sa iya biyan muhimman bukatu kamar kudin makarantar ‘ya’yansu idan sun bar aiki.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa tsohon wakilin Kebbi ta Kudu ya yi gyara a tunanin da wasu ke yi na cewa mallakar kujerar gwamnati tamkar hanyar samun dukiya ce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Halin da tsofaffin ‘yan majalisa ke shiga
Daily Post ta ruwaito cewa tsohon Sanatan ya ce mutane da dama na ganin kujerun gwamnati a matsayin hanyar arziki, amma da zarar sun sauka daga mulki, suna fuskantar matsin rayuwa.
Ya ce:
“Ka koma mazabarka ko wani wuri da ka san akwai masu rike da ofisoshin gwamnati, musamman ‘yan majalisar wakilai da Sanatoci. Ka gaya min wani Sanata da ya bar siyasa na tsawon shekara guda, kuma yana iya biyan kudin makarantar ‘ya’yansa?”
Sanata ya ce tsofaffin ‘yan majalisa na fama
Sanata Na’Allah ya jaddada cewa kallon kitse ake yi wa rogo, musamman ga 'yan majalisar da suka kammala aikinsu.
Tsohon Sanatan ya ce:
“Wasu daga cikinsu sun shiga majalisa da zaton cewar wurin ne da ake tara kudi, amma daga baya suka gano cewa su ma za su fita daga cikinta cikin talauci,."
Ya bayyana cewa ba wai yana kare ‘yan majalisa ba ne, sai dai yana bayani ne bisa abin da ya gani a zahiri.

Asali: Facebook
Na’Allah, wanda ya kasance mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan karo na 8, bai samu nasarar komawa majalisa ba a 2023.
Abokin hamayyarsa, Garba Maidoki ya kayar da shi da kuri’u 75,232 yayin da shi ya samu 70,785.
Rikicin majalaisa kwanan nan
Majalisar Dokoki ta Najeriya na fuskantar manyan kalubale, musamman bayan ‘yan majalisa sun sauka daga mukamansu.
Tsohon Sanata Bala Ibn Na’Allah ya bayyana cewa da yawa daga cikinsu ba sa iya biyan bukatun yau da kullum, ciki har da kudin makarantar ‘ya’yansu.
A cewarsa, ra’ayin cewa zama dan majalisa wata hanya ce ta tara dukiya ba gaskiya ba ne. Ya bayyana cewa wasu sun shiga siyasa da tsammanin arziki, amma daga bisani suka bar ofis cikin matsi da talauci.
Na’Allah, wanda ya wakilci Kebbi ta Kudu a Majalisar Dattawa ta 8, ya ce bayan barin aiki, wasu daga cikin tsofaffin ‘yan majalisa suna shiga mawuyacin hali na rayuwa.
Wannan ya saba da yadda jama’a ke kallon su a matsayin masu kudi da gata. Ya ce gaskiyar al’amari shi ne cewa akwai ‘yan siyasa da dama da ke fama da rayuwa mai wahala bayan sun bar kujerunsu.
Wannan matsala tana nuna bukatar sake duba tsarin albashi da jin dadin wadanda suka taba yin aiki a gwamnatin Najeriya, musamman a majalisa.
Shugaban majalisa ya ce a rungumi talauci
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa talauci ba laifi ba ne, kuma wani lokaci ana kallonsa a matsayin wata falala.
Akpabio ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi ƙaunar juna da haɗin kai, yana mai jaddada cewa talauci bai kamata a duba shi a matsayin mummunan abu ba a tsakanin al'umma.
Akpabio ya yi nazari kan rayuwar marigayi Fafaroma Francis wanda ya rasu yana da shekaru 88, inda ya ba da shawarar jama'a su yi koyi da halayensa na gudun duniya, maimakon tara kudi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng