2027: Atiku zai Yi Amfani da Matasa Miliyan 1.5 domin Kare Kuri'un ADC
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya ce jam’iyyar za ta horar da matasa sama da miliyan 1.5 ta hannun ƙungiyoyin magoya bayanta
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce matasan za su taimaka wajen kare ƙuri’un ADC a rumfunan zaɓe daban-daban a faɗin ƙasar yayin zaɓen 2027
- Atiku Abubakar ya kuma buƙaci ƙungiyoyin magoya bayan jam’iyyar su wayar da kan masu zaɓe tare da guje wa saye da sayar da ƙuri’a a zabe mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce jam’iyyar za ta horar da matasa sama da miliyan 1.5 domin taimakawa wajen kare ƙuri’arta a zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja yayin wani taron tattaunawa da jam’iyyar ta shirya tare da ƙungiyoyin magoya bayanta.

Source: Facebook
Atiku ya nemi a kare ƙuri’u
The Sun ta wallafa cewa Atiku, wanda wani ya wakilta a wajen taron, ya ce zaɓen 2027 zai bai wa ’yan Najeriya wata dama ta sake yin zaben shugabannin da suka dace.
Ya buƙaci shugabannin ƙungiyoyin magoya bayan jam’iyyar su tashi tsaye wajen wayar da kan masu zaɓe a matakin ƙasa d domin samun nasarar ADC.
Sai dai ya gargaɗi magoya bayan jam’iyyar da su guji saye da sayar da ƙuri’u.
Ya ce:
“Ina shawartar ku da ku guji barin a yaudare ku har ku ci amanar lamirinku. Kada ku bari kuɗi da alkawuran APC mai mulki su ruɗe ku.”
An kafa ƙungiyoyin kare ƙuri’u
Tsohon shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, Chief Okey Nwaosu, ya ce jam’iyyar na da aƙalla ƙungiyoyin magoya baya 1,500 da za su taimaka wajen sanya ido kan harkokin zaɓen 2027.
A cewarsa, jam’iyyar na fuskantar matsin lamba daga hukumomin tsaro da ake zargin gwamnatin da ke kan mulki ke da iko da su.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya ki karbar tayin zama abokin takarar Atiku a ADC? An ji gaskiyar zance
Ya ce ba za su daina fafutukar ganin sun samu nasara ba, duk da kalubalen da suke fuskanta.
Alhaji Hashim Imam ya ce ’yan Najeriya sun riga sun yanke shawarar cewa akwai buƙatar sauya gwamnatin APC a 2027.

Source: Facebook
Dino ya gargadi EFCC
Sanata Dino Melaye ya buƙaci Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziƙi Ta’annati, EFCC, da ta daina gayyatar Atiku Abubakar domin yi masa tambayoyi.
A wani bidiyo da ya wallafa a Facebook, Melaye ya ce jam’iyyar ba za ta ƙara lamuntar abin da ya kira yawan musgunawa ɗan takararta ba.
Ya kuma bayyana goyon bayansa ga maido da tallafin man fetur, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage wa ’yan Najeriya wahalhalun rayuwa.
OBi zai kare kuri'un NDC
A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ce jam’iyyarsa za ta kafa tsarin isar da sakamakon zaɓe.
Obi ya ce tsarin zai taimaka wajen tabbatar da cewa an ƙirga ƙuri’u tare da rubuta sakamakon kowace rumfar zaɓe yadda ya kamata.
Ya kuma ce za a riƙa aika sakamakon ta hanyoyi biyu, ɗaya zuwa tashar INEC da aka tanada, ɗayan kuma zuwa cibiyar da jama’a za su iya gani.
Asali: Legit.ng
