Dan Takarar Gwamna Ya Sadaukar da Albashinsa ga Matan da Mazajensu Suka Mutu idan Ya Ci Zabe

Dan Takarar Gwamna Ya Sadaukar da Albashinsa ga Matan da Mazajensu Suka Mutu idan Ya Ci Zabe

  • Ɗan takarar gwamnan jihar Rivers na jam'iyyar NDC, Dumo Lulu-Briggs, ya yi alkawarin bai wa zawarawa albashi da alawus ɗinsa idan ya lashe zaɓen 2027.
  • Dumo Lulu-Briggs ya yi alkawarin ba da albashi da alawus ɗinsa ga Ɗan takarar NDC ya bayyana shirin gudanar da gwamnati bisa gaskiya, riƙon amana da sadaukar da kai ga jama’a
  • Lulu-Briggs ya ce zai iya rayuwa ba tare da albashin gwamnati ba saboda harkokin kasuwancinsa za su ci gaba da tallafa masa bayan barin mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Rivers - Ɗan takarar gwamnan Jihar Rivers na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Dumo Lulu-Briggs, ya yi alkawarin ba da albashi da alawus ɗinsa.

Dan takarar na jam'iyyar NDC ya yi alkawarin bayar da albashin ne ga matan da mazajensu suka mutu a faɗin jihar idan aka zaɓe shi gwamna a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Peter Obi na neman mulkin Najeriya, gwamnatin Anambra ta kunno masa wuta a gida

Lulu-Briggs ya dauko alkawura
Dan takarar gwamnan jihar Rivers na jam'iyyar NDC, Dumo Lulu-Briggs Hoto: Dumo Lulu-Briggs
Source: Facebook

Lulu-Briggs ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da manema labarai da aka gudanar ranar Litinin, 5 ga watan Oktoban 2026 a Buguma, garinsu da ke ƙaramar hukumar Asari-Toru ta jihar, cewar rahoton jaridar The Punch.

A yayin taron, ɗan takarar ya bayyana shirinsa na gudanar da jihar mai taken ‘Reset Rivers State’, wanda ya ce zai mayar da hankali kan sauya fasalin shugabanci da tafiyar da jihar.

Ya ce zai gudanar da gwamnati cikin gaskiya

Lulu-Briggs ya yi alƙawarin kafa gwamnati da za ta dogara kan gaskiya, riƙon amana da sadaukar da kai, tare da samar da yanayin da zai bai wa matasa damar yin manyan bururruka da kuma cimma burinsu.

Ya ce shawarar da ya yanke na sadaukar da albashinsa ta samo asali ne daga ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, wanda ya bayyana a matsayin jagoransa.

“Idan muka samu damar kula da dukiyar gwamnati, zan iya tabbatar wa mutanen Rivers cewa za a yi gaskiya kan kowane kwabo da aka kashe."

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya umarci cafke 'yan 'Tinubu Must Go a Borno'? An ji yadda zancen yake

“Na tabbata zan yi koyi da jagorana, ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi. Ba zan ma nemi albashi ba. Duk wata, albashin zai tafi wajen taimaka wa wata bazawara ko wata.”

Ya ce kasuwancinsa zai tallafa masa

Lulu-Briggs ya ce kasancewarsa mai dogaro da kansa ta fuskar kuɗi zai ba shi damar gudanar da aikin gwamnati ba tare da dogaro da albashin gwamnati ba.

Ya ce harkokin kasuwancinsa za su ci gaba da tafiya ko bayan ya bar kujerar gwamna, lamarin da zai ba shi damar ci gaba da samun abin dogaro.

“Yadda muka tafiyar da abubuwa, ba ma za a buƙaci a biya ni fansho ba, saboda na tabbata kasuwancina za su ci gaba da tafiya.” In ji shi.
Dan takarar NDC a Rivers ya yi alkawura
Dumo Lulu-Briggs a wajen taron jam'iyyar NDC Hoto: Dumo Lulu-Briggs
Source: Facebook

Dan takarar da ya fi cancanta ya zama shugaban kasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam’iyyar PRP, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Donald Duke, shi ne ya fi kowane dan takara cancanta a zaben 2027.

Ya ce tsohon gwamnan na jihar Cross River yana da nagarta da cancantar jagorantar Najeriya fiye da sauran masu neman kujerar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng