Har da N298,000: Ana Korafi bayan Jami'ar ABU Ta Kara Kudin Makarata

Har da N298,000: Ana Korafi bayan Jami'ar ABU Ta Kara Kudin Makarata

  • Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta ƙara kuɗin rijistar ɗalibanta na zangon karatu na 2026/2027, inda wasu za su biya har N298,000
  • Sabon tsarin ya nuna cewa kuɗin da ɗalibai za su biya ya tashi daga N143,000 zuwa N298,000, gwargwadon fanni da matakin karatu
  • Ƙarin kudin ya jawo suka daga ƙungiyar NANS da wasu ɗalibai, yayin da hakan ya sake tayar da fargabar yiwuwar ƙarin kuɗin karatu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, ta amince da sabon tsarin kuɗin rijistar ɗalibai wanda zai fara aiki daga zangon karatu na 2026/2027.

Sabon tsarin ya nuna gagarumin ƙari daga N62,000 zuwa N84,000 da ɗalibai suka biya a zangon karatun da ya gabata.

Jami'at ABU Zariya
Kofar shiga jami'ar ABU Zariya. Hoto: ABU Zaria
Source: Twitter

Jami'ar ABU ta wallafa sanarwar karin kudin ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Shugaban Amurka ya ɗora laifin abin da ke faruwa a Faransa kan addinin Musulunci

Sabon tsarin kuɗin makarantar ABU

A sabon tsarin, ɗaliban ilmin likita 'yan shekarar farko za su biya N242,000, bayan kuɗin ya tashi daga N82,000.

Daliban likitancin hakori su ma za su biya N242,000 daga N82,625, yayin da ɗaliban shari'a za su biya N182,000 maimakon N82,625 da ake biya a baya.

A fannonin injiniynci daban daban, kuɗin dalibai 'yan ajin farko ya tashi zuwa N172,000 daga N82,625.

Haka kuma, ɗaliban da ke karantar ilmin jinya da sauran masu alaka da su za su biya N212,000, bayan kuɗin ya tashi daga N78,875.

Sauran karin kudin da aka yi

Kuɗin karatu a fannin duba lafiyar dabbobi ya tashi zuwa N232,000 daga N82,625, yayin da ɗaliban ilmin komfuta za su biya N172,000 maimakon N82,625.

A bangaren Akawu, Ilmin Tsimi da sauransu kuwa, kuɗin 'yan ajin farko ya tashi zuwa N152,000 daga N75,125.

A cewar jadawalin da jami’ar ta amince da shi, ɗalibai za su biya tsakanin N143,000 zuwa N298,000, gwargwadon fannin karatu da matakin da suke.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa NADECO ya riga mu gidan gaskiya

NANS da ɗalibai sun yi martani

Ƙarin kudin ya jawo ce-ce-ku-ce daga ɗalibai da wasu ’yan Najeriya, yayin da shugaban ƙungiyar National Association of Nigerian Students (NANS), Akinteye Afeez, ya bayyana matakin a matsayin abin da ya wuce wasa.

Premium Times ta wallafa cewa Afeez ya ce idan shugaban jami’ar ba zai iya gudanar da makarantar yadda ya kamata ba, ya kamata ya yi murabus.

Taswirar jihar Kaduna
Taswirar jihar Kaduna a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Wasu ɗalibai ma sun bayyana rashin jin daɗinsu a shafukan sada zumunta, inda suka koka kan yadda ake ci gaba da ƙara kuɗin karatu.

ASUU ta tallafa wa dalibar jami'a

A wani labarin, mun ruwaito cewa Maryam Umar, mai shekaru 26 da aka haife ta ba tare da hannaye biyu ba, ta kammala karatu a Jami’ar Jihar Gombe.

Maryam ta samu tallafin karatu na N1.68m daga Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU), bayan wallafa labarin irin ƙalubalen da ta fuskanta wajen samun damar ci gaba da karatu.

Maryam wadda ke rubutu da yin ayyukan gida da yatsun ƙafafunta, ta samu gurbin karatu ne bayan ta kammala sakandare a 2022 tare da samun maki 182 a jarabawar UTME.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng