Ke Duniya: Karamin Yaro Ya Bankawa Gidan Mahaifinsa Wuta don Ramuwar Gayya, an Rasa Rayuka
- ’Yan sanda sun kama wani yaro mai shekaru tara bisa zargin banka wa gidan mahaifinsa wuta a Karasuwa, Yobe, inda mutane huɗu suka mutu
- Ana zargin yaron ya aikata hakan ne domin ramuwar gayya bayan mahaifinsa ya hukunta shi saboda ya sace wata kaza domin sayarwa
- Yaron ya shaida cewa ya sayi ashana ta N50, ya kunna wutar yayin da matan mahaifinsa biyu da ’yan uwansa biyu suke barci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Yobe - Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta kama wani yaro mai shekaru tara bisa zargin banka wa gidan mahaifinsa wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar uwayensa mata biyu da ƙannensa biyu.
Lamarin ya faru ne a Rugan Badal, wani ƙaramin ƙauye da ke Ƙaramar Hukumar Karasuwa ta Jihar Yobe.

Source: Original
An ce ya yi hakan ne domin ramuwar gayya
Jaridar Daily Trust ta ce a cewar ’yan sanda, ana zargin yaron ya banka wa gidan su wuta ne domin ɗaukar fansa kan mahaifinsa bayan ya hukunta shi saboda satar kaza.
Yaron ya bayyana dalilin da ya sa ya aikata hakan a wata hira da tashar Channels Tv. Ya ce ya ɗauki ɗaya daga cikin kajin gidan domin sayarwa, amma wasu mutane suka kai rahotonsa ga mahaifinsa saboda shekarunsa.
A cewarsa, mahaifinsa ya yi masa duka saboda wannan abu na satar kaza da ya aikata.
“Na ɗauki ɗaya daga cikin kajinmu domin sayarwa. Jama’a, ganin shekaruna, suka kai rahoto ga mahaifina, sai ya buge ni."
“Washegari, na sayi ashana ta N50 a unguwa, yayin da matan mahaifina biyu da ƙannena biyu suke barci. Sai na banka wa gidanmu wuta domin ɗaukar fansa kan abin da mahaifina ya yi mini,” in ji shi.
Wutar ta kashe mutane huɗu
Wutar ta bazu cikin sauri a gidan, inda waɗanda abin ya shafa ta ritsa da su. Yaron ya ce bayan ya kunna wutar, ya ɗaga murya yana neman taimako domin jawo hankalin maƙwabta.

Kara karanta wannan
Ana jimamin hatsarin sojoji, fasinja ya mutu a jirgin da ke kan hanyar zuwa Legas
Sai dai ya ce bai bayyana cewa shi ne ya kunna wutar ba a lokacin.
“Lokacin da gidan ya kama da wuta, na yi ihu ne kawai ina neman taimako, sai mutane suka zo domin ceto."
“Ban gaya musu cewa ni ne na yi hakan ba sai bayan an yi addu’a na tsawon kwanaki uku. Daga nan na faɗi gaskiya, daga baya ’yan sanda suka kama ni suka kawo ni Damaturu,” in ji shi.
’Yan sanda sun gabatar da yaron da mahaifinsa
Rundunar ’Yan Sandan Yobe ta gabatar da yaron tare da mahaifinsa, Abubakar Idi, a ranar Talata, 6 ga watan Oktoban 2026.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, ASP Yusuf Adamu-Ali, ya bayyana cewa wanda ake zargin ƙaramin yaro ne.
Sai dai ya ce girman laifin da ake zargin yaron da aikatawa na buƙatar a bi matakan da doka ta tanada, domin hakan ya zama darasi ga sauran mutane.
Lamarin ya girgiza al’ummar yankin
Lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin jimami, tare da haifar da tambayoyi kan yadda ake ladabtar da yara, yanayin tunaninsu da kuma sauƙin samun abubuwan da za su iya jawo hatsari.
A halin yanzu, rundunar ’yan sanda na ci gaba da bincike domin gano cikakken bayani game da abin da ya faru.

Source: Twitter
Malamin jami'a ya mutu a otel
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani babban malami a Jami’ar Ambrose Alli da ke Ekpoma, Jihar Edo, Dr. Matthew Uwuigbe, ya mutu a otel bayan sun yi lalata da karuwa.
Uwuigbe ya shiga otel ɗin tare da matar mai suna Angela Defa Jacob, inda daga baya ya faɗi ya mutu a cikin ɗakin.
Asali: Legit.ng

