Malamin Addini Ya Dauki Zafi, Ya Ce Za a Iya Kashe duk Wanda Ya Saci Akwatun Zabe a 2027
- Babban limamim coci, Fasto Chibuzor Chinyere, ya gargadi matasan Najeriya kan yiwuwar rasa rayukansu idan suka yi yunƙurin satar akwatin zaɓe a 2027
- Ya ce zamanin satar akwatunan zaɓe ya kamata ya ƙare yayin da Najeriya ke shirin gudanar da zaɓe na gaba
- Malamin ya kuma ƙalubalanci ’yan siyasar da ake zargi da amfani da matasa wajen tayar da tarzoma a lokacin zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Fitaccen malamin coci kuma wanda ya kafa Omega Fire Ministry, Apostle Chibuzor Chinyere, ya gargadi matasan Najeriya kan satar akwatun zabe a lokacin babban zaben 2027.
Faston ya bayyana cewa matasa za su iya rasa rayukansu idan suka yi yunƙurin satar akwatin zaɓe a babban zaɓen da ke tafe.

Source: Facebook
Chinyere ya bayar da wannan gargaɗin ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafin X, inda ya ce ya kamata a kawo ƙarshen satar akwatunan zaɓe yayin da ’yan Najeriya ke shirin shiga zaɓe na gaba.

Kara karanta wannan
Nigeria @66: Cikakken jawabin da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a ranar samun 'yancin kai
Chinyere ya gargadi matasa
Malamin ya kuma ƙalubalanci ’yan siyasar da ake zargi da amfani da matasa wajen tayar da tarzoma a lokacin zaɓe da su dawo da ’ya’yansu ƙasar domin su shiga aikin satar akwatunan zaɓe.
A cewar malamin addinin kiristan, ’yan siyasa da dama na tura matasa su shiga rikicin zaɓe yayin da ’ya’yansu ke zaune a ƙasashen waje suna hutawa ko kuma suna karatu.
Ya ce ya kamata matasan Najeriya su ƙi yarda a yi amfani da su wajen aiwatar da muradun ’yan siyasa, yana mai kira gare su da su buƙaci ’ya’yan irin waɗannan ’yan siyasa su shiga ayyukan da ake zargin iyayensu na ƙarfafa su.
Fasto ya nemi a daina satar akwatu
Da yake gargadin matasa a cikin faifam bidiyon da ya wallafa, Fasto Chinyere ya ce:
“To gare ku dukkan matasan Najeriya, a zaɓen 2027, idan kuka kusanci wani akwatin zaɓe da niyyar sace shi kawai, za ku mutu.
“Babban zaɓen 2027 ba zai sake kasancewa kamar zaɓukan baya ba saboda ’yan Najeriya sun gaji. Zamanin satar akwatin zaɓe ya ƙare, ya wuce, ya zama tarihi.
“Har yaushe ’yan Najeriya za su ci gaba da yaudarar kansu tare da barin ’yan siyasa su yaudare su? Suna da ’ya’ya, kuma ’ya’yansu suna ƙasashen waje. Su dawo da ’ya’yansu su sace musu akwatunan zaɓe."

Source: Facebook
Malamin coci ya yi nasiha kan zabe
A wani labarin, kun ji cewa malamin addinin Kirista, Fasto Enoch Adeboye ya bayyana cewa Allah ya riga ya zabi shugaban Najeriya na gaba kafin zaben 2027, yana cewa ikon Ubangiju ya fi karfin siyasa.
Adeboye ya ce sakamakon zabe ba abu ne da mutane kadai za su iya tantancewa ba, domin nufin Allah shi ne zai tabbata a karshe.
Malamin addinin ya bayyana cewa bai taba hana Kiristoci shiga siyasa ba, amma dole mutane su fahimci cewa Ubangiji ne ke da ikon karshe a harkokin rayuwar bil’adama.
Asali: Legit.ng
