Gwamna Buni Ya Fadi Alkawarin da Suka Yi da Kudu kan Zaben Tinubu a 2027
- Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya bayyana cewa zaɓen Shugaba Bola Tinubu a wa'adi na biyu al'amari ne na adalci da cika alƙawari
- Buni ya bukaci mutanen Arewa da su mutunta yarjejeniyar karɓe-karɓen mulki kamar yadda Kudu ta ba su damar yin shekaru takwas
- Shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa Inuwa Yahaya da Alhaji Kabiru Masari sun yaba da shigar mata malamai cikin harkokin siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kaduna – Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana cewa mutunta yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin Arewa da Kudu kan karɓe-karɓen shugabanci zai tabbatar da adalci tare da ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu damar yin da wa'adi na biyu.
Gwamna Buni ya bayyana hakan ne a garin Kaduna a ranar Lahadi yayin da yake jawabi a taron ƙungiyar malamai mata da malaman jami'a.

Kara karanta wannan
Tinubu na ta samun goyon baya a Arewa, manyan malaman jami'o'i 600 sun bayyana matsayarsu

Source: Facebook
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mamman Mohammed ya fitar a Facebook, ta bayyana cewa Buni ya jaddada buƙatar ba Tinubu damar kammala shirye-shiryen da ya faro.
Buni ya ce a zabi Tinubu
A bayanin da Buni ya yi, ya buƙaci mahalarta taron da su tsaya tsayin daka wajen tabbatar da gaskiya ta hanyar ba yankin Kudu damar mulki ta tsawon shekaru takwas kamar yadda Arewa ta yi.
Ya rubuta cewa:
"Ya kamata batun adalci da gaskiya ya shafi kowane fanni, kuma ina farin ciki da shigar malaman Islama cikin tsarin siyasa domin tsayawa a kan tafarkin gaskiya da kuma haɓaka siyasar Najeriya."
Kira ga malamai da shugabanni
Gwamnan ya roƙi malaman da su isar da wannan saƙo zuwa jihohinsu daban-daban, inda ya bayyana cewa malamai suna da babbar rawar da za su taka wajen tabbatar da zaman lafiya tun daga matakin unguwanni har zuwa matakin ƙasa baki ɗaya.
Shi ma a nasa ɓangaren, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Al'amuran Siyasa, Alhaji Kabiru Masari, ya yaba wa malaman bisa sha'awar da suka nuna wajen ciyar da siyasar ƙasar gaba, inda ya buƙace su da su goyi bayan zaɓen Tinubu a karo na biyu.

Source: Facebook
Haka zalika, Gwamnan jihar Gombe kuma shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Alhaji Inuwa Yahaya, ya bayyana shigar matan malaman Islama cikin siyasa a matsayin abin a yaba la'akari da rawar da suke taka wa wajen gina al'umma.
Maganar Zulum kan Tinubu
A wani labarin, mun rahoto cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da haƙuri da ƙoƙarin gwamnatin tarayya wajen shawo kan matsalolin tsaro, talauci da sauran ƙalubale.
Zulum ya yi wannan kiran ne a garin Kaduna biyo bayan taron da ya gudanar da mata malamai na Arewa, inda ya bayyana cewa shugabannin Arewa sun cimma matsaya ta goyon bayan tazarcen Shugaba Bola Tinubu.
Gwamnan ya ƙara da cewa an ɗauki wannan mataki ne tsakanin shugabannin domin dorewar haɗin kai da kuma tabbatar da cewa mulkin ya koma yankin Arewa bayan kammala wa'adin na Tinubu.
Asali: Legit.ng
