Duk da Sace Malamai Maza, Malaman Addini Mata Sun Goyi Bayan Tinubu
- Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bayyana dalilin da ya sa malaman addinin Musulunci mata daga jihohin Arewa 19 suka amince da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Uba Sani ya ce malaman sun yanke wannan shawarar ne saboda nasarorin da Tinubu ya samu da kuma tsarin mulkinsa na bai wa kowane yanki dama
- Uba Sani ya ce musamman bangaren ilimi, kiwon lafiya, noma da ayyukan more rayuwa ne suka sa malaman suka bayyana goyon bayansu ga shugaban kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bayyana dalilin da ya sa malamai mata na Arewa suka amince da sake tsayawa takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki daga jihohin Arewa 19 da aka gudanar a Kaduna ranar Lahadi.

Source: Facebook
Mata sun goyi bayan Tinubu
The Cable ta rahoto Uba Sani ya ce wakilan malaman mata da suka halarci taron suna wakiltar miliyoyin mambobinsu a fadin Arewa.
Ya ce sun bayyana goyon bayansu ga Tinubu ne ta bakin shugabanninsu, ba wai saboda son rai ko wata manufa ta kashin kai ba.
Ya ce:
“Ba su goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne saboda son zuciya ko wata manufa ta kashin kai ba. Abin da suka yi la’akari da shi shi ne abubuwan da ya yi wa Najeriya da Arewa musamman.”
Batun ilimi da cigaba
Gwamnan ya ce malaman sun yaba wa Tinubu saboda irin ci gaban da ya samu a bangarorin ilimi, ayyukan more rayuwa, kiwon lafiya da noma.
A cewarsa, tsarin shugabancin Tinubu na bai wa kowane bangare na Najeriya dama ya kasance abin a yaba.

Source: Twitter
Uba Sani ya ce malaman sun bayyana cewa Tinubu yana tafiyar da mulki cikin adalci, yana kuma kai ayyukan ci gaba zuwa sassa daban-daban na kasar ba tare da nuna wariya ba.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Gwamnoni, Malamai da manyan Arewa sun yi taro, sun yiwa Tinubu mubaya'a
NELFUND da TVET a Arewa
Premium Times ta wallafa cewa gwamnan ya ce cikin shekaru uku da rabi, gwamnatin Tinubu ta zuba jari sosai ba kawai a tsarin ilimi na yau da kullum ba, har ma da ilimin koyon sana’o’i.
Ya ce shirye-shiryen koyar da sana’o’i da fasahohi na TVET da kuma tallafin Asusun Ba da Lamunin Ilimi ga ’Yan Najeriya, NELFUND, sun taimaka wa Arewa sosai.
A cewarsa, bayanan da ke kan manhajojin NELFUND da TVET sun nuna cewa Arewa ta samu sama da kashi 60 cikin 100 na amfanin shirye-shiryen.
Uba Sani ya ce hakan ya nuna cewa Tinubu mutum ne da bai nuna wariya tsakanin kabilu ko yankuna ba, kuma ya yi imani da Najeriya daya.
Kiran Zulum ga 'yan Arewa
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya bukaci ‘yan Najeriya su yi hakuri da kokarin gwamnatin tarayya na magance matsalar tsaro, talauci da sauran kalubalen kasar.

Kara karanta wannan
Abdulaziz Yari ya fadi sirri da ya kama aikin tallar Tinubu babu kama hannun yaro
Zulum ya bayyana hakan ne a Kaduna bayan wani taron tattaunawa da malamai mata na Arewa da malaman addinin Musulunci.
Gwamnan ya ce shugabannin Arewa sun amince da goyon bayan Tinubu a wa’adi na biyu, tare da fahimtar cewa daga baya mulki zai koma Arewa.
Asali: Legit.ng
