2027: Zulum Ya Ce Mulki zai Dawo Arewa, Ya Fadi Lokaci
- Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya bukaci ’yan Najeriya su yi haƙuri da gwamnatin Bola Tinubu wajen magance matsalolin tsaro da talauci
- Zulum ya ce shugabannin Arewa sun amince su mara wa Tinubu baya a zaɓen 2027, bisa fahimtar cewa bayan wa’adinsa mulki zai koma Arewa
- Gwamnan ya ce yarjejeniyar siyasar Arewa da Kudu na da muhimmanci wajen tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya tsakanin yankunan biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno – Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya yi magana kan tsarin rabon mulki tsakanin Arewa da Kudancin Najeriya da kuma zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Zulum ya ce shugabannin Arewa sun yanke shawarar mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a ƙoƙarinsa na neman wa’adi na biyu, da fahimtar cewa mulki zai koma Arewa bayan ya kammala wa’adinsa.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Gwamnoni, Malamai da manyan Arewa sun yi taro, sun yiwa Tinubu mubaya'a

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a Kaduna, bayan wani taron tattaunawa da ya yi da malaman mata na Arewa da malaman addinin Musulunci.
Yarjejeniyar Arewa da Kudu
Zulum ya ce shugabannin Arewa sun kuduri aniyar cika alkawuran da aka yi wa shugabannin Kudancin Najeriya kan tsarin juyin mulki tsakanin yankunan biyu.
Ya ce matakin na da nufin ƙarfafa haɗin kai da kuma tabbatar da zaman lafiya tsakanin Arewa da Kudu.
Gwamnan ya ce:
“Kimanin shekaru biyar da suka wuce, mun yanke shawarar tabbatar da haɗin kan Arewa, kuma mun cimma wannan buri.”
Trust Radio ya wallafa cewa ya ƙara da cewa Arewa ta mara wa Tinubu baya wajen samun mulki, don haka ya kamata a ci gaba da mutunta fahimtar siyasar da aka cimma tsakanin yankunan biyu.
Batun kira a yi hakuri
Zulum ya bukaci ’yan Najeriya su mara wa gwamnatin Tinubu baya domin ta samu damar aiwatar da manufofinta da shirye-shiryenta.

Kara karanta wannan
An fara fito da abubuwan da Tinubu ya shirya yi a Najeriya idan ya lashe zaben 2027
Ya ce shugabannin Arewa sun tattauna matsalolin tsaro, yara marasa zuwa makaranta da talauci a wani taro da manyan ’yan yankin suka gudanar.
A cewarsa, an cimma wasu muhimman shawarwari domin magance matsalolin da ke addabar yankin da inganta rayuwar al’ummarsa.

Source: Facebook
Zulum ya ce a yi hakuri
Zulum ya ce zaman lafiya shi ne babban burin al’ummar Arewa, yana mai cewa mutane na ci gaba da addu’ar ganin an kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro.
Ya bukaci mata su yi haƙuri, yana mai cewa koyarwar Musulunci ta tabbatar da muhimmancin haƙuri yayin fuskantar jarrabawa.
Ya ce:
“Idan Allah Ya jarrabe mu da wata fitina, haƙuri ya zama dole kafin samun sauƙi.”
Zulum ya ce ya kamata Arewa ta yi haƙuri ta bar Kudu ta kammala wa’adinta, yayin da suke aiki tare domin tsara makomar siyasar yankin.
INEC ta kare Tinubu a kotu
A wani labarin, mun ruwaito cewa INEC ta bukaci Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da ke zargin Shugaba Bola Tinubu da gabatar da takardun bogi.
Hukumar ta ce ƙarar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar ADC, Atiku Abubakar, ya shigar ta kasance cin zarafi ga tsarin shari’a.
INEC ta kuma ce Atiku ba shi da ikon shigar da ƙarar, tana mai cewa batutuwan da aka gabatar a cikinta zato ne kawai kuma ba su da isasshen dalilin ci gaba da shari’ar.
Asali: Legit.ng
