Zaben 2027: Omokri Ya Gano 'Sirrin' da Zai Yi Tasiri kan Shugaba Tinubu
- Reno Omokri ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaɓen 2027 da gagarumin rinjaye
- Ya ce Tinubu yanzu yana da goyon bayan gwamnonin jihohi da dama, musamman a Arewa, fiye da lokacin zaɓen 2023
- Omokri ya yi iƙirarin cewa wasu dalilan da suka jawo ƙuri’un adawa da Tinubu a 2023 ba za su yi tasiri iri ɗaya a zaɓen 2027 ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jakadan Najeriya da aka naɗa zuwa Mexico, Reno Omokri, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya riga ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Omokri ya yi hasashen cewa Tinubu zai lashe zaɓen da “gagarumin rinjaye”, yana mai cewa shugaban ya ƙara ƙarfafa matsayinsa na siyasa tun bayan zaɓen 2023.

Source: UGC
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da Seun Okinbaloye a shirin Politics Today na Channels Tv.
Omokri ya kwatanta 2023 da 2027
Omokri ya ce matsayin Tinubu a siyasar Najeriya yanzu ya fi ƙarfi idan aka kwatanta da lokacin da ya fafata a zaɓen 2023.
Ya ce a wancan lokacin Tinubu na fuskantar ƙalubale da dama, ciki har da rashin kyakkyawar alaka da gwamnatin tarayya, manufar canjin kuɗi da kuma hamayyar manyan ’yan adawa. Ya ce duk da waɗannan ƙalubalen, Tinubu ya samu nasarar lashe zaɓen.
“Mafi kyawun abin da ke hasashen abin da zai faru a nan gaba shi ne abin da ya faru a baya,” in ji shi.
Omokri ya ƙara da cewa a yanzu Tinubu na kan kujerar shugaban ƙasa kuma yana da goyon bayan kusan gwamnonin jihohi 30.
Ya ambaci goyon bayan Tinubu a Arewa
Jakadan da aka nada ɗin ya kuma yi nuni da tarukan siyasar da aka gudanar a Katsina da Kano a matsayin alamar ƙara samun karɓuwar Tinubu a Arewacin Najeriya.
Ya tambayi ko an ga yawan mutanen da suka halarci tarukan, yana mai cewa hakan na nuna irin goyon bayan da shugaban ke samu a yankin.
Ya ambaci Atiku da Peter Obi
Omokri ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, na daga cikin manyan abokan hamayyar Tinubu a 2027.
Ya ce a Adamawa, inda Atiku ya fito, gwamna mai ci da tsohon gwamna suna goyon bayan Tinubu tare da gudanar da tarukan neman masa goyon baya.
Haka kuma, ya yi nuni da Anambra, jihar da Peter Obi ya fito, yana mai cewa gwamnan jihar na goyon bayan Tinubu.

Source: Getty Images
Omokri ya yi magana kan 'yan takara
A wani labarin kuma, kun ji cewa Reno Omokri, ya ce akwai bayanan dukkan ’yan takarar shugaban kasa a zaben 2027 a Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka (FBI).
Reno Omokri ya ce kasancewar mutum yana da bayanai a hukumar FBI ba yana nufin yana da tarihin aikata laifi ba.
Omokri ya ce wajibi ne ’yan Najeriya su fahimci bambanci tsakanin bayanan da FBI ke da su kan mutum da kuma tarihin aikata laifi.
Asali: Legit.ng

