Matakin da PRP Za Ta Ɗauka kan Zargin Sanata Shehu Buba da Ta'addanci
- Jam’iyyar PRP ta kare Sanata Shehu Buba kan zargin alakarsa da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane
- PRP ta ce ta tabbatar zarge-zargen wani shiri ne na bata sunan ɗan takararta gabanin zaɓen 2027, saboda karuwar farin jininsa
- Jam’iyyar ta yi barazanar daukar matakin shari’a, tana mai cewa dokar zaɓe ta 2026 ta tanadi hukunci kan yada bayanan ƙarya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Jam’iyyar PRP ta yi watsi da zarge-zargen alakanta ɗan takararta na gwamnan Bauchi, Sanata Shehu Buba, da ayyukan ‘yan bindiga.
Jam’iyyar ta ce tun farko ta kauracewa mayar da martani ga zarge-zargen, saboda ba ta son ba su damar samun karin karbuwa.

Source: Facebook
A wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran Kasa na jam’iyyar, Kwamared Muhammed Ishaq, ya fitar ranar Asabar, PRP ta ce zarge-zargen ba su da tushe, cewar Vanguard.
Ta'addanci: PRP ta kare Sanata Shehu Buba
Sai dai PRP ta ce a yanzu ta fahimci cewa zarge-zargen wani shiri ne na bata sunan Sanata Buba gabanin zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta ce ta yi shiru ne domin ta fara bincike tare da tabbatar da sahihancin zarge-zargen da ake yi wa ɗan takararta.
Sanarwar ta ce:
“PRP ta yi tsayin daka wajen kin yin tsokaci kan zarge-zargen da ke kara kamari, wadanda ke alakanta ɗan takararmu na gwamna da ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa.
“Jam’iyyar ta guji shiga muhawara da wadanda ke yada wadannan zarge-zarge na son zuciya, saboda damuwar cewa hakan zai kara bai wa wannan shiri damar samun karfi.”
PRP ta ce daga bisani ta cimma matsayar cewa zarge-zargen ƙarya ne, kuma an shirya su ne domin rage karfin siyasar Sanata Buba.
Jam’iyyar ta zargi wasu mutane da ke ganin cewa farin jinin Sanata Buba da damar da yake da ita ta zama gwamnan Bauchi na gaba na barazana gare su.
“PRP yanzu ta gamsu cewa akwai wani shiri na lalata sunan ɗan takararmu ta hanyar tarin ƙarya da makirci marar iyaka.
“Yanzu mun yi imanin cewa wadanda ke jin barazana daga farin jinin ɗan takararmu da damar da yake da ita ta zama gwamnan Bauchi ne suka kitsa wadannan zarge-zarge.”
- Cewar sanarwar
PRP ta kalubalanci duk wanda ke da hujjar aikata laifi kan Sanata Buba da ya gabatar da ita ga hukumomin da suka dace, maimakon yada zarge-zarge marasa tushe.
Ta ce:
“Dole ne a daina yada wdannan ƙaryace-ƙaryacen. Duk wanda ke da hujjar aikata wani laifi a kansa ya gabatar da ita ga hukumomi, wadanda za su yi aiki da ita bisa doka.”
Jam’iyyar ta kuma yi nuni da tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026, tana gargadin cewa yada bayanan ƙarya kan halayya ko ayyukan ɗan takara na iya jawo hukunci.
PRP ta musamman ambaci sashe na 127(c) na dokar, wanda ta ce ya haramta yada bayanan ƙarya game da halayya ko ayyukan ɗan takara ba tare da ingantacciyar hujja ba.

Kara karanta wannan
Halin da ake ciki da yan sanda suka tabbatar da hari kan ayarin motocin Peter Obi
A cewar jam’iyyar, wanda aka samu da laifin na iya fuskantar tarar N200,000, zaman gidan yari na watanni shida ko kuma hukuncin biyun, cewar Punch.
PRP ta ce wannan tanadi ya dace da halin da ake ciki, musamman yayin da zaɓen 2027 ke kara matsowa da zarge-zargen da take kira masu cutarwa ke karuwa.
Jam’iyyar ta dage cewa tarihin Sanata Buba da matsayinsa a idon jama’a ba su goyi bayan zarge-zargen da ake yada wa kansa.
Ta kuma zargi abokan hamayyarsa na siyasa da masu sukar sa da amfani da “ƙarya mai muni da bata suna” saboda karuwar tasirin Sanatan a siyasa.
“Mun yi imanin cewa abokan hamayyarsa da masu sukar sa suna jin barazana saboda yaduwa da zurfin farin jininsa, don haka suka koma yada ƙarya mai muni da bata suna a kansa.”
PRP ta bukaci masu adawa da takarar Sanata Buba su fafata da shi ta hanyar siyasa, maimakon amfani da abin da ta kira yakin bata suna.
Hadimin Shehu Buba ya yi murabus
A wani labarin, an ji cewa babban mataimakin majalisa na Sanata Shehu Buba Umar, ya yi murabus daga mukaminsa bayan zarge-zargen ta'addanci.

Kara karanta wannan
Janar Christopher Musa ya kira ruwa, lauyoyin El Rufai sun nemi N10bn da wasu bukatu
Murabus din Tilde ya zo ne a yayin da ake sabunta zargin alakanta Sanata Shehu Buba da ’yan bindiga da ta’addanci.
Tilde ya ce ya yanke shawarar barin aikin ne bayan wasu abubuwa da suka hada da rashin sanar da shi taron da sanatan ya gudanar.
Asali: Legit.ng

