Janar Musa Ya Kira Ruwa, Lauyoyin El Rufai Sun Nemi N10bn da Wasu Bukatu

Janar Musa Ya Kira Ruwa, Lauyoyin El Rufai Sun Nemi N10bn da Wasu Bukatu

  • Lauyoyin Malam Nasir El-Rufai, sun nemi N10bn daga Christopher Musa saboda zargin yin kalaman ɓata suna kan tsohon gwamnan
  • Lauyoyin sun zargi Janar Musa da cewa ya danganta El-Rufai da kashe-kashe a Kudancin Kaduna, biyan ’yan bindiga da rushe gidaje
  • Tawagar lauyoyin ta ce ba a taɓa tabbatar da zarge-zargen a gaban kotun da ta dace ba, inda ta bukaci ministan ya kawo hujjoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Lauyoyin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, sun nemi diyyar N10 biliyan daga Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya).

Lauyoyin na tsohon gwamnan jihar Kaduna sun bukaci diyyar ne bisa zargin ɓata sunan wanda suke wakilta.

Lauyoyin El-Rufai sun yi barazana ga Janar Musa
Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa da Malam Nasir El-Rufai Hoto: Ministry of Defence Nigeria
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta ce an bayyana buƙatar a cikin wasiƙar gargaɗi kafin shigar da ƙara, mai dauke kwanan wata 7 ga Satumba, 2026, wadda aka aika wa Janar Musa a ma’aikatar tsaro ta tarayya da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: Iyalan El Rufai sun yi martani mai zafi ga Janar Christopher Musa

Matakin ya biyo bayan bayyanar ministan a shirin Politics Today na Channels Tv ranar 3 ga Satumba, 2026.

Zarge-zargen da aka yi wa El-Rufai

A cewar wasiƙar, lauyoyin sun ce Janar Musa ya zargi El-Rufai da shirya kashe mutane a Kudancin Kaduna da gangan, tare da biyan ’yan bindiga.

Sun kuma yi zargin cewa ministan ya ce El-Rufai ya ba da umarnin rushe gidaje, inda ake amfani da irin waɗannan matakai wajen hukunta abokan hamayyarsa.

Lauyoyin El-Rufai, wato Akpan Ubong Chambers, sun bayyana kalaman a matsayin ƙarya da kuma masu ɓata suna.

Sun ce zarge-zargen sun nuna tsohon gwamnan a matsayin mai aikata laifi, kisa da kuma ɗaukar nauyin ’yan bindiga, Leadership ta kawo rahoton.

An nemi N10bn da neman afuwa

Lauyoyin sun buƙaci Ministan Tsaro ya janye kalaman a bainar jama’a tare da ba El-Rufai haƙuri.

Baya ga hakan, sun nemi a biya tsohon gwamnan N10 biliyan a matsayin diyya kan abin da suka bayyana a matsayin illar da kalaman suka haifar wa mutuncinsa.

Kara karanta wannan

Dalung ya jefawa Christopher Musa tambayoyi kan zargin Nasir El Rufa'i

Game da zargin biyan ’yan bindiga, lauyoyin sun musanta hakan, suna cewa El-Rufai ya sha bayyana cewa ba zai taɓa tattaunawa ko biyan kuɗi ga ’yan bindiga ba.

Sun kare matakin rushe gidaje

Lauyoyin sun kuma yi watsi da zargin cewa rushe-rushe da aka gudanar a lokacin mulkin El-Rufai a Kaduna sun kasance don musgunawa abokan hamayya.

A cewarsu, rushe-rushen da aka yi a lokacin mulkinsa an gudanar da su ne bisa tanadin doka da kuma wasu manufofin da suka shafi amfanin jama’a.

Haka kuma, sun ƙaryata zargin cewa gwamnatin El-Rufai ta raba Kaduna bisa ƙabilanci da addini. Sun ce manufofin gwamnatin sun kasance ne da nufin inganta haɗin kan jama’a da ci gaban jihar.

Lauyoyin sun nemi hujjoji

Tawagar lauyoyin ta jaddada cewa babu wani daga cikin zarge-zargen da aka gwada ko tabbatar da shi a gaban kotun da ke da hurumin yanke hukunci.

Saboda haka, sun buƙaci a gabatar da cikakkun hujjoji da za su tabbatar da kalaman da aka yi kan tsohon gwamnan.

Matakin na ƙara jawo hankali kan takaddamar da ta kunno kai tsakanin magoya bayan El-Rufai da Ministan Tsaro kan kalaman da suka shafi tsaro da abubuwan da suka faru a Kaduna.

Kara karanta wannan

APC ta shiga matsala, manyan jam'iyya sun fita za su fara adawa da Tinubu

Lauyoyin El-Rufai sun taso Janar Musa a gaba
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

Martanin iyalan El-Rufai ga Janar Musa

A wani labarin kuma, kun ji cewa iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai sun yi wa Janar Christopher Musa martani.

Iyalan tsohon gwamnan sun bukaci Ministan tsaron da ya janye kalamansa tare da bayar.da hakuro ko kuma su maka shi kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng