Ana tsaka da Zargin Shehu Buba da Ta'addanci, Hadiminsa Ya Yi Murabus
- Babban mataimakin majalisa na Sanata Shehu Buba Umar, ya yi murabus daga mukaminsa bayan zarge-zargen ta'addanci
- Murabus din Tilde ya zo ne a yayin da ake sabunta zargin alakanta Sanata Shehu Buba da ’yan bindiga da ta’addanci, zargin da ya musanta
- Tilde ya ce ya yanke shawarar barin aikin ne bayan wasu abubuwa da suka hada da rashin sanar da shi taron da sanatan ya gudanar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Zargin Sanata Shehu Buba kan alaka da yan ta'adda ya fara daukar sabon salo a Najeriya bayan rasa wani hadiminsa.
Babban hadiminsa a bangaren Majalisa, Hon. Abba Aliyu Tilde, ya yi murabus daga mukaminsa bayan shafe tsawon lokaci suna tare.

Source: Facebook
Wakilin Legit Hausa ya samu wannan bayani ne daga shafin Abba Aliyu Tilde wanda ya wallafa a Facebook a yau Talata.
Tilde ya bayyana cewa an samu matsala wajen mutunta juna, sadarwa da amana a tsakaninsa da sanatan Bauchi ta Kudu.
Tilde ya sanar da murabus dinsa ne cikin wata wasika mai kwanan watan 6 ga Satumba, 2026, inda ya ce murabus din zai fara aiki nan take.
Martanin Shehu Buba kan zargin ta'addanci
Murabus din ya zo ne a yayin da aka sake sabunta zarge-zargen da ke alakanta Sanata Shehu Buba da ayyukan ’yan bindiga da ta’addanci, zarge-zargen da sanatan ya sha musantawa.
Buba ya bayyana zarge-zargen a matsayin kirkirarru, masu alaka da siyasa, kuma wani yunkuri ne na bata masa suna.
Sababbin zarge-zargen sun biyo bayan yaduwar wasu bidiyoyi da ikirarin da aka wallafa a kafafen sada zumunta, wadanda ke cewa wasu da ake zargi da jagorantar ’yan bindiga sun kai ziyara gidan sanatan.
Sai dai Buba ya yi watsi da wadannan abubuwa, yana mai cewa an yi amfani da dabarun sauya ko shirya su, sannan ya ce ya dauki matakin shari’a kan mutanen da ke yada abin da ya kira yakin bata suna.

Source: Facebook
Musabbabin murabus din Aliyu Tilde
Sai dai a cikin wasikar murabus dinsa, Tilde bai zargi sanatan da hannu a wadannan zarge-zargen ba, kuma bai alakanta murabus dinsa kai tsaye da wannan batu ba.
Maimakon haka, ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne saboda abin da ya bayyana a matsayin sake watsi da shi da kuma rashin nuna godiya ga rawar da yake takawa.
Musamman, ya ambaci wata ziyara da Sanata Buba ya kai mazabarsa, inda aka gudanar da wani taro da mazauna yankin ba tare da an sanar da shi ba.
Ya ce:
“Saboda matsayina da kuma alakar da nake da ita da mutanen wannan mazaba, na ji wannan abu a matsayin babban rashin mutuntawa da kuma abin da ya cutar da zuciyata. Na yi imanin cewa, a kalla, ya kamata a sanar da ni kuma a hada ni cikin lamarin."
Ya ce abin da ya faru, tare da wasu abubuwan da ya fuskanta, ya sa ba zai iya ci gaba da gudanar da aikinsa yadda ya kamata a irin wannan yanayi ba.
Tilde ya ce ya yi imanin cewa kowace irin alakar aiki, musamman wadda ta shafi siyasa da hidimar jama’a, ya kamata ta kasance bisa mutuntawa, aminci da kuma yarda da aikin mutum.
“Abin takaici, yanzu ba na jin cewa wadannan ka’idoji suna cikin alakar aikinmu, ba zan iya ci gaba da kasancewa a matsayin da nake jin ba a mutunta gudummawar da nake bayarwa ko kuma alakar da ke tsakaninmu."
- Aliyu Tilde
Tilde ya nuna godiyarsa kan damar da aka ba shi ta yi wa sanatan aiki a matsayin Babban Mataimakin Majalisa, sannan ya yi masa fatan samun nasara a ayyukansa na gaba.
Karin bayani na tafe ....
Asali: Legit.ng


