‘Abin Tsofaffin Shugabanni Ke Tsoro Tinubu Ya Aiwatar domin Tausayin ’Yan Kasa’
- Ministan Ma’adanai, Dele Alake, ya bayyana irin nuna kwarin guiwa da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Najeriya
- Alake ya ce gwamnatocin baya sun kasa cire tallafin saboda tsoron zabe, yayin da tsarin ya fi amfanar dillalan man fetur
- Ministan ya bukaci a ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki, yana cewa matakan sun fara haifar da sakamako mai kyau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Ma’adanai, Dele Alake, ya bayyana irin sadauarwa da Shugaba Bola Tinubu ya yi game da siyasa a Najeriya.
Alake ya ce Tinubu ya sadaukar da siyasarsa wajen cire tallafin man fetur domin farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Source: Facebook
Alake ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ‘yan jaridun APC a Abuja, inda ya ce gwamnatocin baya sun kasa daukar wannan mataki, cewar Punch.
Yadda gwamnatocin bayan suka gagara cire tallafi
Ya ce gwamnatocin baya sun fahimci bukatar cire tallafin, amma suka jinkirta saboda tsoron zabe da illar siyasa da matakin zai iya haifarwa.
Alake, wanda aka nada daraktan dabarun sadarwa na yakin neman zaben Tinubu na 2027, ya ce shugaban ya yanke shawarar daukar nauyin matakin.
Ya ce babu lokacin da ya dace gaba daya wajen daukar tsauraran matakan tattalin arziki, don haka dole ne shugabanni su dauki matakin da ya dace.
A cewarsa, tsarin tallafin man fetur ya fi amfanar dillalan man fetur da masu hannu da shuni, yayin da gwamnati ta rasa kudaden zuba jari.
Ya ce manufofin da ake bukata domin gyara matsalolin tattalin arziki sun kasance sanannu tun a gwamnatocin baya, amma abin da ya rasa shi ne karfin gwiwar daukar matakin.
Ya ce:
“Babu wata hanya ta gajarta wajen yin gyare-gyare na gaskiya. Ba sai na yi bayani kan irin halin da tattalin arzikin Najeriya yake ciki kafin 2023 ba.
“Babu wata hanya ta gajarta. Dattawanmu suna cewa idan kana cikin rami, me za ka yi? Ka daina kara tona shi. Domin duk yadda ka ci gaba da tonawa, zurfin da za ka shiga yana karuwa.”

Source: Twitter
Ya ce gwamnatocin baya sun kasa dakatar da wannan matsala saboda son cimma bukatun siyasa na gajeren lokaci da kuma tsoron zabe.
Matsalolin da cire tallafin mai ya jawo
Ministan ya tuna yadda batun cire tallafin man fetur ya jawo zanga-zanga a baya, inda gwamnati ta koma baya kan matakin saboda zabe na gabatowa.
Alake ya ce Bola Tinubu ya zo ne ya yanke shawarar “shanye wannan kwayar daci” tare da daukar nauyin illolin matakin a madadin ‘yan Najeriya.
Ministan ya ce ya kamata a yaba wa Tinubu saboda ya dauki hadarin siyasa, ba tare da la’akari da illar hakan ga makomar siyasarsa ba, cewar Daily Post.
Tinubu ya roki fastoci kan siyasar 2027
A wani labarin, an ji cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bukaci shugabannin Kirista su yi amfani da mimbari wajen yaɗa zaman lafiya.
Tinubu ya ce shugabannin addini su yi kira ga jama’a su guji sayen ƙuri’a, kalaman ƙiyayya da amfani da ƙabila ko addini.
Kungiyar shugabannin Kirista ta bayyana goyon bayanta ga Tinubu a zaben 2027, tana cewa za ta ci gaba da mara masa baya.
Asali: Legit.ng

