An Yi Jina Jina da Sojoji Suka Gwabza Fada da 'Yan Ta'adda, an Rasa Rayuka

An Yi Jina Jina da Sojoji Suka Gwabza Fada da 'Yan Ta'adda, an Rasa Rayuka

  • Rundunar Operation Hadin Kai ta kashe ’yan ta’adda 16 a wani samame da sojoji suka kai kan sansanin ’yan ta’adda a yankin Boima da ke Gombi a Adamawa
  • Rundunar Sojin Najeriya ta kuma tabbatar da mutuwar sojoji uku yayin wasu hare-haren ’yan ta’adda da suka faru a sansanonin soji da ke Garkida da Garaha
  • Hare-haren da kuma ayyukan sojin sun faru ne tsakanin 30 ga Satumba da 1 ga Oktoba, 2026, inda aka kuma kwato makamai da alburusai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Adamawa – Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ’yan ta’adda 16 a wani kwanton bauna da suka shirya a yankin Boima da ke ƙaramar hukumar Gombi ta jihar Adamawa.

Rundunar ta kuma ce ta yi asarar sojoji uku yayin wasu hare-haren ’yan ta’adda da aka kai a sansanonin soji da ke Garkida da Garaha.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya ya yi kamari: Gwamnatin Tinubu ta nemo dabarun yaki da cutar

Sojojin Najeriya a bakin aiki
Dakarun sojin Najeriya a Kwara. Hoto: Kwara State Government
Source: Facebook

An kashe ’yan ta’adda 16

The Cable ta wallafa cewa jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin gwiwar sojoji ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce dakarun sun kai samamen ne tsakanin 30 ga Satumba da 1 ga Oktoba.

Ya ce dakarun sun shirya kwanton bauna kan sansanin ’yan ta’adda a yankin Boima, inda suka yi nasarar kashe wasu daga cikin mayakan.

Bayan artabun, sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku, bindigogin pump-action guda biyu, bindiga ƙirar Dane guda ɗaya, harsasai shida na AK-47 da sauransu.

An farmaki 'yan ta'adda

Kyaftin Goni ya ce rundunar sama ta Operation Hadin Kai ta kuma kai wani hari ta sama da safiyar 1 ga Oktoba bayan na’urar leƙen asiri ta gano tarin ’yan ta’adda.

A cewarsa, da misalin ƙarfe 4:40 na safe ne aka gano kusan ’yan ta’adda 16 da ke taruwa tare da babura 15 a ƙarƙashin bishiyoyi a wani yanki na Sector 4.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda sun fadi hakikanin dalilin kama masu sanye da rigar #TinubuMustGo

Ya ce bayan tabbatar da wurin da suke, jirgin ya kai hari da misalin ƙarfe 5:30 na safe, inda aka samu nasarar auka wa wurin da aka nufa.

Rundunar ta ce binciken da aka gudanar bayan harin ya tabbatar da lalacewar wurin da aka kai wa harin, yayin da wasu daga cikin waɗanda suka tsira suka watse cikin rudani.

An kashe sojoji 3

A gefe guda, Punch ta wallafa cewa Goni ya ce ’yan ta’adda sun kai hare-hare a lokaci guda kan sansanonin sojoji da ke Garkida da Garaha.

Ya ce sojojin sun mayar da martani da ƙarfin wuta, inda suka fatattaki maharan tare da tilasta masu janyewa.

Sai dai ya ce sojoji uku sun rasa rayukansu yayin gumurzun, yayin da aka kwashe wasu sojojin da suka jikkata zuwa asibiti domin kulawa kuma suke cikin kwanciyar hankali.

Taswirar jihar Adamawa
Taswirar jihar Adamawa a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

An kai karin sojoji Zamfara

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da sababbin bataliyoyin sojojin ƙasa guda uku a jihar Zamfara.

Sababbin bataliyoyin sun haɗa da 12 Infantry Battalion da ke Bakura, 23 Infantry Battalion da ke Kaura Namoda da kuma 28 Infantry Battalion da ke Anka.

Rundunar ta ce sabbin bataliyoyin za su faɗaɗa wuraren da sojoji ke gudanar da ayyuka tare da ƙara kare yankunan da aka ɗora musu alhakin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng