Dan Takarar Shugaban Kasa Zai Mayar da Litar Fetur N200, Ya Fadi Abin da Ya Shirya

Dan Takarar Shugaban Kasa Zai Mayar da Litar Fetur N200, Ya Fadi Abin da Ya Shirya

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP, Adewole Adebayo, ya yi alkawarin rage farashin man fetur, gas da Jet A1 zuwa N200 kan lita
  • Adebayo ya ce za a cimma hakan cikin watanni 12 ta hanyar farfaɗo da matatun mai da samar da yanayin da matatun mai ƙanana za su bunƙasa
  • Ya kuma yi alkawarin rage kuɗin sufuri da gidaje, tare da samar da ilimi da kiwon lafiya kyauta idan SDP ta samu mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Prince Adewole Adebayo, ya yi alkawarin rage farashin man fetur.

Adewole Adebayo ya yi alkawarin rage farashin man fetur da gas ɗin girki da man jiragen sama Jet A1 zuwa N200 kan lita idan aka zaɓe shi a 2027.

Adebayo zai rage farashin fetur
Dan takarar shugaban kasa na SDP, Adewole Adebayo Hoto: Prince Adewole Adebayo
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce Adebayo ya bayyana hakan ne ranar Lahadi, 6 ga watan Satumban 2026 a Abuja yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya shirya.

Kara karanta wannan

"Na samu labari mara dadi"; Atiku ya haska matsalar da matasa ke fuskanta a gwamnatin Tinubu

Ya ce za a cimma hakan cikin shekara guda

Ɗan takarar ya ce gwamnatinsa za ta cimma wannan buri cikin watanni 12 ta hanyar farfaɗo da matatun man Najeriya tare da samar da yanayin da zai ba matatun mai na zamani masu ƙanana damar bunƙasa.

Adebayo ya ce matatun man Najeriya, waɗanda yawancinsu ba su kai shekaru 50 ba, har yanzu suna da damar aiki kuma za su iya samar da man da ƙasar ke buƙata.

Ya kwatanta hakan da Amurka, inda ya ce wasu matatun mai da suka haura shekaru 100 har yanzu suna aiki.

Ya yi alkawarin dawo da tsarin tallafin mai

Adebayo ya kuma ce zai dawo da tsarin tallafin man fetur na baya, wanda ya ware ganga 450,000 na ɗanyen mai domin amfanin cikin gida.

A cewarsa, za a sayar da sauran abubuwan da ake samu daga wannan ɗanyen mai, kamar naphtha, heavy fuel oil, dizal da kananzir, sannan a yi amfani da kuɗin wajen daidaita farashin man.

Kara karanta wannan

Da hannun gwamnatin Najeriya a yunkurin juyin mulki a Nijar? An gano gaskiya

Ya soki muhawarar cire tallafin mai

Ɗan takarar shugaban ƙasar ya ce muhawarar da ake yi yanzu kan tallafin man fetur na kawar da hankalin jama’a daga manyan matsalolin da ke addabar ɓangaren man fetur na Najeriya.

Ya ce abin da ya kamata ƙasar ta fi mayar da hankali a kai shi ne samar da isasshen ƙarfin tace ɗanyen mai a cikin gida, maimakon ci gaba da shigo da tataccen mai daga ƙasashen waje kan farashin duniya.

Adebayo ya ce Najeriya na da babbar dama saboda tana da ɗanyen mai da kuma matatun mai, don haka ya kamata ta riƙa tace mai a cikin gida.

SDP za ta rage farashin kayayyakin man fetur

A cewarsa, gwamnatin SDP za ta sanya gas ɗin girki, man fetur da Jet A1 cikin tsarin da farashinsu ba zai wuce N200 kan lita ba.

“SDP za ta ɗauki gas ɗin girki, man fetur da Jet A1; waɗannan ukun za mu sanya su cikin tsarin da farashinsu ba zai wuce N200 ba,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Amaechi ya fadi tallafin da Atiku zai sake dawo da shi bayan na man fetur

Adebayo zai rage farashin man fetur a Najeriya
Adewole Adebayo na daga hannu a wajen taro Hoto: Prince Adewole Adebayo
Source: Facebook

An goyi bayan dawo da tallafin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban jam'iyyar ADC na kasa, Ralph Nwosu, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya yi kuskure wajen cire tallafin man fetur.

Nwosu ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya nuna jajircewa da karfin hali ta hanyar bayyana cewa zai dawo da tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng