'Abin da Ya Sa Nake So Ƴan Najeriya Su Sake Zaɓen Tinubu': Oluremi

'Abin da Ya Sa Nake So Ƴan Najeriya Su Sake Zaɓen Tinubu': Oluremi

  • Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta roƙi ’yan Kudu maso Gabas su sake zaɓar mijinta, Bola Tinubu, a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
  • Oluremi Tinubu ta ce tana son ganin Najeriya ta inganta kafin ta tsufa, yayin da ta bayyana cewa ita da shugaban ƙasa suna aiki don cigaban ƙasar
  • Uwargidan shugaban ƙasar ta ƙarfafa mata 2,500 a Imo da kayan sana’a, sannan ta sanar da ƙarin tallafin N100,000 ga kowacce daga cikin waɗanda suka amfana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Owerri, Imo — Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta roƙi yan Najeriya su goyi bayan sake zaɓen mijinta, Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Uwargidan shugaban ƙasar ta ce tana son jin daɗin Najeriya mai kyau a lokacin tsufa, tana mai cewa ita da shugaban ƙasa suna ƙoƙarin inganta ƙasar.

Kara karanta wannan

Da gaske ma'aikatan gwamnatin tarayya sun nemi ƙarin albashi domin zaben APC?

Sanata Oluremi Tinubu ta roki yan Najeriya kan tazarcen Tinubu
Sanata Oluremi Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Senator Oluremi Tinubu.
Source: Twitter

Oluremi Tinubu ta yi wannan roƙon ne ranar Laraba a Owerri, babban birnin Imo, yayin ziyarar aiki da ta kai yankin Kudu maso Gabas domin ƙarfafa mata, cewar Vanguard.

Shirin Oluremi kan inganta rayuwar mata

Uwargidan shugaban ƙasar ta ce ana aiwatar da shirin ƙarfafa matan ne ta Ofishin Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Manufofin Cigaba Mai ɗorewa, SDGs.

Ta ce shirin zai amfani mata 18,500 a faɗin ƙasar idan aka kammala shi, yayin da mata 500 daga kowacce jiha biyar na Kudu maso Gabas za su samu kayan sana’a.

Ya ce:

“Ku zaɓi Tinubu, za mu yi aiki domin ku kuma Najeriya za ta inganta, ina son jin daɗin Najeriya a lokacin tsufa, saboda haka zan yi aiki domin Najeriya, domin lokacin tsufana."
Oluremi ta bukaci yan Najeriya su zaɓi Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

Kayayyakin da Oluremi ta raba

Ta ce kayan da za a raba sun haɗa da janareto, injinan nika na masana’antu, silindar gas da murhu, domin taimaka wa mata wajen gudanar da sana’o’insu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ware gwamna a Arewa ya kwararo masa yabo

Sai dai ta bayyana cewa Gwamnan Imo, Sanata Hope Uzodimma, ya samar da ƙarin kayan tallafi ga mata 2,000 a jihar, cewar Punch.

Hakan ya sa adadin matan da za su amfana da shirin a Imo ya koma 2,500, inda Tinubu ta ƙara sanar da tallafin N100,000 ga kowacce.

Ta ce an tsara shirin ne domin amincewa da muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen gina ƙasa da bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya.

“Idan aka yi la’akari da irin rawar da mata ke takawa wajen gina ƙasa, wannan ya yi daidai da ajandar Mista Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
“Ajandar ta ba da fifiko ga bunƙasar tattalin arziƙi da cigaba mai ɗorewa ga dukkan ’yan Najeriya, musamman mata."

- In ji ta.

Oluremi Tinubu ta shawarci waɗanda suka amfana da shirin da su yi amfani da kayan da tallafin da aka ba su yadda ya kamata.

Oluremi ta tallafawa yan Najeriya

Mun ba ku labarin cewa uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, za ta je wata jiha a Najeriya inda za ta ƙarfafa haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da jihar.

Kara karanta wannan

Daliban Najeriya sun kama layi, sun faɗi yadda Tinubu ya inganta rayuwarsu

Uwargidar za ta ƙaddamar da shirin tallafa wa mutane 5,000, domin rage talauci da inganta rayuwar iyalai masu buƙata.

Haka kuma, za ta ƙaddamar da Bankin Abinci na Al’umma na ƙasa a Kudu maso Gabas, sannan ta ƙaddamar da wasu ayyuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.