Ministan Tsaro Ya Sa Majalisar Kolin Harkokin Musulunci ta Dauki Zafi a Shari’ar El Rufai

Ministan Tsaro Ya Sa Majalisar Kolin Harkokin Musulunci ta Dauki Zafi a Shari’ar El Rufai

  • NSCIA ta fito ta yi maganar shari’ar Nasir El-Rufai sakamakon kalaman da Ministan Tsaro ya yi a kansa
  • Janar Christopher Musa (mai murabus) ya zargi El-Rufai da haifar da rashin tsaro a Kudancin Kaduna
  • Majalisar ta yi gargadin cewa dole a yi adalci a kotu kuma kada a bar mutane su hura wutar rigima a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - Majalisar kolin harkokin Musulunci a Najeriya ta gargadi gwamnatin tarayya game da shari’ar Nasir El-Rufai.

NSCIA ta kuma yi wa alkalai kashedi cewa ka da su bari wasu mutane su yi amfani da addini a shari’ar da ake yi a kotu.

El-Rufai
Malam Nasir El-Rufai tare da wani fasto da hoton tsohon gwamnan yana addu'a Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Facebook

Aminiya ta rahoto majalisar tana zargin cewa abubuwan da suka bayyana kwanan nan sun nuna kamar da lauje cikin nadi.

An ji Ministan tsaro, Janar C. G Musa mai ritaya ya fito yana cewa Nasir El-Rufai ya gallaza wa wasu da yake karagar mulki.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta shiga Aso Rock ta dauke ma’aikacin da ya yi aiki da shugabannin kasa 3

Hakurin NSCIA ya kare a shari'ar Nasir El-Rufai

Majalisar ta yi bakin kokarin ta na ganin ba ta ce komai game da shari’ar El-Rufai ba, sai dai yanzu dole ta fitar da jawabi.

Wannan ne karon farko da aka ji NSCIA da ke karkashin Sarkin Musulmi ta tsoma baki a lamarin tun watan Maris na shekarar nan.

Jawabin ya fito ne ta bakin Sakataren NSCIA na kasa, Farfesa Is-haq Oloyede a ranar Talatar nan, 8 ga watan Satumba 2026.

Majalisar tana tsoron a yi amfani da addini

Tsoron Farfesa Oloyede shi ne manufar addini tana iya tasiri a boye a shari’ar da ICPC da DSS suke yi da tsohon gwamnan Kaduna.

Ministan tsaro ya ce lokacin da El-Rufai yake ofis, ya kawo matsaloli a Kaduna har ya zarge shi da kitsa kashe kiristoci a jihar.

Duk da an dade ana fama da rikicin addini a Kaduna, CG Musa ya alakanta lamarin da El-Rufai, wanda hakan ya jawo masa suka.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Abin da El Rufai ya fada da aka nada Janar Musa Ministan Tsaro

El-Rufai: Kiran NSCIA ga alkalai da jama'a

Saboda haka NSCIA ta yi kira ga bangaren shari’a da a tabbata ba a nuna son kai a karar ba, ko a yi amfani da sabani na addini.

This Day ta ce majalisar ta gargadi sauran al’ummar gari da su kaurace wa sakin baki, su yi maganganun da za su kawo matsala.

Haka zalika farfesan ya yi karin haske cewa ba su neman a fasa shari’ar, illa dai suna so ne alkalai su yi wa babban ‘dan adawar adalci.

A karshe jawabin ya yi addu’ar Allah SWT ya samar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya yayin da 'dan siyasar yake hannun ICPC.

El-Rufai
Tsohon gwamna Nasir El-Rufai lokacin yakin zaben 2023 a Kaduna Hoto: @AishaUmmi_Garba
Source: Twitter

Majalisar shari'a da batun tsare El-Rufai

Wannan matsaya ta zo daidai da ta Majalisar shari’a wanda Sheikh Bashir Aliyu Umar yake jagorantar kamar yadda aka labarta.

Ita ma ta bakin Nafiu Baba-Ahmed, ta yi kira ga wadanda abin da ya shafa su tabbata an yi adalci kuma ba a nuna wani son kai ba.

SCSN ta jaddada cewa El-Rufai mai gaskiya ne har sai kotu ta same shi da laifi, sannan ta yi kiran a kiyaye martabar doka da ta ɗan adam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng