Tarihin arziki na: Atiku ya bayyana yadda ya fara kasuwanci tun shekarar 1971
Atiku Abubakar hamshakin mai-kudi ne a cikin jerin 'yan siyasar Najeriya, kuma ga ddukkan alamu, ma'aikacin gwamnati ne a dduk rayuwarsa, shi ta yaya ya tara makudan kudadensa? Ya amsa cewa ba ta hanyar satar kudin gwammnati ya tara kudinsa ba, wai ddabaru ne na neman kudi da iya kasuwanci suka azurta shi.

Atiku Abubakar, a jiya, ya ce ya fara kasuwancinsa da sayen gingimari guda hudu ta dako, inda ya ke kasuwancinsa, tare da aikinsa na kwastan a lokacin yana sanya khaki.
A littafinsa kuwa, My Life, cewa yayi gidajen haya ne ya gina yake karbar haya. Da ma kuma kasuwanci da yace sun faro shi da Shehu Yaraduwa, lokacin yana shigo dda wake daga Nijar.
DUBA WANNAN: Dubi da wa Najeriya zata kara a gasar kwallon kofin Duniya
Atikun dai, yana neman takarar shugabanci ne a matakin tarayya, amma bai bayyana ko a wacce jam'iyya zai tsaya ba.
Sai ma ya kira samari da su tashi tsaye su nemi arziki, kada su bari zaman banza ya kashe musu jiki. Tace tun 29 ga watan Yuni ta 1969 ya koma Legas da zama a kwastam.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng