Daliban Najeriya Sun Kama Layi, Sun Faɗi yadda Tinubu Ya Inganta Rayuwarsu

Daliban Najeriya Sun Kama Layi, Sun Faɗi yadda Tinubu Ya Inganta Rayuwarsu

  • Kungiyar daibai ta NANS ta ce wasu manufofin Shugaba Bola Tinubu, ciki har da rancen karatu da inganta jin daɗin ɗalibai
  • Shugaban NANS Akinteye Afeez ya ce ɗalibai suna bibiyar manufofin gwamnati da tasirinsu ga karatu da jin daɗinsu
  • Akinteye ya bayyana cewa NANS na shirin wayar da kan ɗalibai tare da neman goyon bayansu ga Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS) ta danganta wasu sabbin ci gaba a fannin ilimi da jin daɗin ɗalibai da manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Ƙungiyar ta kuma bukaci ɗalibai su yi la’akari da tasirin waɗannan manufofi yayin da zaɓen shekarar 2027 ke gabatowa, ba tare da la’akari da ra’ayinsu ba.

Dalibai sun yaba wa Tinubu kan inganta rayuwarsu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yana jawabi a taro. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Shugaban NANS, Akinteye Afeez, ya bayyana hakan ne a wani taro tsakanin wakilan ƙungiyar ɗaliban da jami’an APC Youth Network West Africa, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan gudun hijira a Kano ba ta son ganin Ali Modu Sheriff a gangamin yakin neman zaben APC

Yadda Tinubu ya taimakawa daliban Najeriya

Akinteye ya bayyana Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND), ingantacciyar wutar lantarki a wasu jami’o’i da raguwar yajin aikin ma’aikatan ilimi.

Ya ce waɗannan sauye-sauyen na iya taimakawa wajen inganta yanayin karatu da rayuwar ɗaliban Najeriya a jami’o’i da sauran manyan makarantun ƙasa.

Ya bayyana cewa ɗaliban Najeriya suna sa ido sosai kan manufofin gwamnati da tasirinsu ga ilimi da jin daɗinsu, ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasa ba.

A cewarsa, ɗalibai suna da sha’awar bibiyar duk wani ci gaba da ya shafi karatunsu, rayuwarsu da jin daɗinsu kai tsaye.

Dalibai sun yabawa Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yana tafi a wurin taro. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Albishir da shugaban NANS ya yi ga dalibai

Shugaban NANS ya ce zai isar da batutuwan da aka tattauna a taron ga ɗalibai a faɗin ƙasar domin su kasance cikin sanin abin da ake ciki.

Ya ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da cewa ɗalibai sun fahimci abubuwan da gwamnati ke yi da kuma tasirinsu ga rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Tsakanin Atiku da Obi waye zai iya ƙalubalantar Tinubu? an fadi wanda ya zo da gaske

Akinteye ya kuma bayyana goyon bayansa ga gwamnatin Tinubu, inda ya bayyana shirin tattara ɗalibai domin su marawa Shugaban ƙasar baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Rahotanni sun ce ƙungiyar na da burin samun kuri’u miliyan 10 daga ɗalibai da magoya bayanta domin tallafa wa Tinubu.

Taron ya kuma mayar da hankali kan jin daɗin ɗalibai, ci gaban ilimi, shigar matasa cikin harkokin gwamnati da ayyukan ɗalibai da ake gudanarwa.

An kuma tattauna yiwuwar ƙulla haɗin gwiwa tsakanin shugabannin ɗalibai da APC Youth Network West Africa domin inganta rayuwar matasa.

Dalibai sun ba Tinubu gudunmawar miliyoyi

An ji cewa wasu daliban da suka ci gajiyar shirin NELFUND sun nuna farin cikinsu game da tallafi daga gwamnatin Bola Tinubu.

Daliban sun bayyana goyon baya ga shugaba Bola Tinubu domin ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.

Sun kuma tara Naira miliyan 10.7 domin taimaka wa Tinubu wajen sayen fom din nuna sha’awar tsayawa takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.