Oluremi Tinubu Ta Ware Jiya 1 a Najeriya, Za Ta Yaye wa Mutane 5,000 Talauci

Oluremi Tinubu Ta Ware Jiya 1 a Najeriya, Za Ta Yaye wa Mutane 5,000 Talauci

  • Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, za ta je wata jiha a Najeriya inda za ta ƙarfafa haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da jihar
  • Uwargidar za ta ƙaddamar da shirin tallafa wa mutane 5,000, domin rage talauci da inganta rayuwar iyalai masu buƙata
  • Haka kuma, za ta ƙaddamar da Bankin Abinci na Al’umma na ƙasa a Kudu maso Gabas, sannan ta ƙaddamar da wasu ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Awka, Anambra - Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, za ta ziyarci Anambra ranar Alhamis, 10 ga Satumba, 2026.

Majiyoyi suka ce wannan ziyara an shirya ta ne domin tallafa wa marasa karfi a jihar domin rage masu radadin talauci.

Oluremi Tinubu za ta raba wa mutane 5,000 tallafi
Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu tana jawabi a taro. Hoto: Senator Oluremi Tinubu.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa daga Daniel Ezeigwe, mai taimaka wa matar Gwamnan Anambra, Dr Nonye Soludo, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

2027: Dawo da tallafin mai da alkawura 6 da Atiku ya yi wa talakawa

Oluremi Tinubu za ta ba da tallafi

Sanarwar ta ce haɗin gwiwar ya shafi shirye-shiryen rage talauci, tallafa wa tattalin arziki, samar da abinci da inganta rayuwar marasa galihu a jihar.

Babban abin da zai fi jan hankali yayin ziyarar shi ne shirin tallafa wa mutane 5,000 karkashin shirin APC na rage talauci a kasa.

Shirin ya kasance haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnatin jihar da shirin Renewed Hope Initiative na Uwargidan Shugaban Ƙasa, musamman tsarin tallafin tattalin arziki.

“An tsara shirin tallafin ne domin samar wa waɗanda za su amfana da tallafin tattalin arziki da dama da za su inganta rayuwarsu, musamman masu buƙatar taimako.
“Wani babban abin da zai kasance cikin shirin ziyarar shi ne ƙaddamar da Bankin Abinci na Al’umma na ƙasa a Kudu maso Gabas.”
Oluremi Tinubu za ta je Anambra
Taswirar Anambra da Oluremi Tinubu ke shirin kai ziyara. Hoto: Legit.
Source: Original

Tallafin da aka shirya wa alumma

Sanarwar ta ce za a gudanar da ƙaddamar da shirin a jihar a ranar da Uwargidan Shugaban Ƙasar za ta ziyarci Anambra, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

2027: An fadi wanda ya kamata yan adawa su tsayar takara tsakanin Atiku da Obi

“Shirin wani ɓangare ne na ƙoƙarin Renewed Hope Initiative na ƙarfafa samar da abinci da tallafa wa iyalai masu rauni, musamman saboda ƙarin damuwa kan yunwa.
“Ziyarar Uwargidan Shugaban Ƙasar ta zo ne a daidai lokacin da ake samun ci gaba wajen haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da Anambra.”

- Cewar sanarwar

Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yayin ziyarar da ya kai Anambra ta ƙarshe, ya bayyana alaƙar gwamnatin tarayya da jihar a matsayin haɗin gwiwa.

Ya kuma bayyana cewa haɗin gwiwar ya ginu ne kan moriyar jama’a tare da yabawa irin saurin ci gaban da gwamnatin Gwamna Chukwuma Soludo ke samu.

Sanarwar ta ce dubban mazauna jihar ne ake sa ran za su amfana kai tsaye daga shirin tallafin da sauran tsare-tsaren da aka shirya yayin ziyarar.

'Ku inganta talaka': Tinubu ga gwamnoni

A wani labarin, an ji cewa gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana sane da irin wahalhalun da 'yan Najeriya ke fuskanta sakamakon sauye-sauyensa.

Gwamnan ya ce duk da cewa wasu muhimman alamomin tattalin arzikin Najeriya suna samun sauki, tasirin hakan bai kai ga talakawa da sauran 'yan kasa ba tukuna.

Sule ya ce Tinubu ya umurci gwamnonin jihohi da su kara mayar da hankali kan ayyukan karkara, samar da ruwa, wutar lantarki da shirye-shiryen tallafa wa jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.