Da Gaske Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Sun Nemi Ƙarin Albashi domin Zaben APC?
- Wani binciken ya gano gaskiya kan rahoton cewa ma’aikatan gwamnatin tarayya sun nemi ƙarin albashi domin su zaɓi APC ba
- Ma’aikatan sun nemi a ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N300,000, yayin da suka bukaci N1.5m ga jami’ai da suka kai mataki na 17
- An bayyana cewa ikirarin ma’aikatan sun sharɗanta ƙarin albashi da zaɓen APC a 2027 yaudara ce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Yayin da ake saura kimanin watanni huɗu kafin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki, an fara yada karairayi a Najeriya.
Kwanan nan, wani saƙo ya yadu a kafafen sada zumunta, yana ikirarin cewa ma’aikatan gwamnatin tarayya sun nemi a ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N300,000.

Source: Facebook
Rahoton da aka yi ta yadawa
Saƙon wanda shafin Igbere TV ya saka a Facebook ya ƙara da cewa ma’aikatan sun ce fadi hakan a matsayin sharadin zaɓen jam’iyyar APC a babban zaɓen 2027.
Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun sake yaɗa wannan ikirari a shafukansu, lamarin da ya sa mutane da dama suka fara yarda da bayanin.
A ɓangaren sharhi, Dubawa ya lura cewa wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun yarda da ikirarin, yayin da wasu suka yi tambaya kan manufarsa.
Wani mai amfani mai suna Oliver Nwachukwu ya ce ma’aikata suna da ’yancin neman ƙarin albashi, amma ya gargadi ma’aikata kada su sayar da ƙuri’unsu.
Ya ce bai kamata ma’aikata su musanya ƙuri’unsu da alkawuran ƙarin albashi ba, yana mai cewa ya kamata su zaɓi shugabanni bisa cancanta da gaskiya.

Source: Twitter
Gaskiyar rahoton da ake yadawa
Saboda muhimmancin batun a lokacin da siyasar 2027 ke ƙara ɗaukar hankali, Dubawa ta gudanar da bincike domin tantance sahihancin wannan ikirari.
An ce ma'aikatan sun bukaci karin albashi da samar da shirye-shirye na musamman domin kula da ma'aikatan da jin dadinsu.

Kara karanta wannan
Dan takarar shugaban kasa ya gano abin da ya hana a magance rashin tsaro a Najeriya
Sai dai, ma’aikatan ba su danganta waɗannan buƙatu da zaɓen 2027 ba a cikin sanarwar da suka fitar ga jama’a.
Ikirarin cewa ma’aikatan gwamnatin tarayya sun nemi ƙarin albashi a matsayin sharadin zaɓen jam'iyyar APC a 2027 yaudara ce.
Gaskiya ne ma’aikatan sun nemi a sake duba tsarin albashinsu, amma ba su danganta wannan bukata da zaɓen 2027 ba kamar yadda aka yi ikirari.
Dan takarar shugaban kasa ya tsoratar da APC
Mun ba ku labarin cewa dan takarar shugaban ƙasa na SDP, Adewole Adebayo, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba wanda ba za a iya kayarwa ba ne a zaɓen 2027.
Adebayo ya ce APC za ta zo ta ƙarshe, yana mai cewa sakamakon zaɓen zai dogara ne kan ƙuri’un da ’yan Najeriya za su jefa.
Ɗan takarar ya ce Najeriya na da damar noma da za ta iya ba Afirka abinci, amma rashin isasshen jari ya hana bunƙasar fannin.
Asali: Legit.ng
