'Abin da ADC Ke Gadara da Shi a Zamfara domin Kawar da APC a Zaɓen 2027'
- Shugaban ADC na Zamfara, Kabiru Garba, ya ce jam’iyyar na da ƙarfin da za ta kawar da APC daga mulki a zaɓen 2027
- Garba ya bayyana cewa ADC na ƙara samun karɓuwa a tsakanin al’ummar Zamfara saboda amincewar jama’a da manufofin jam’iyyar
- Ya buƙaci ‘yan takara da magoya bayan ADC su kasance masu natsuwa, bin doka, zaman lafiya tare da sauraron matsalolin masu zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Shugaban jam’iyyar ADC na Zamfara, Kabiru Garba, ya yi magana kan zaben 2027 da ke tafe.
Garba ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar za ta iya kawar da APC mai mulki a zaɓen 2027.

Source: Original
Garba ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Gusau ranar Juma’a, inda ya dage cewa ADC na da abin da ake bukata don kwace mulki a Zamfara a 2027, cewar PM News.
Ya ce idan aka yi la’akari da farin jini, ƙarfi da haɗin kan jam’iyyar a jihar, “tana da ikon kawar da APC daga mulki a Zamfara a babban zaɓen 2027.
Ya ce jam’iyyar na ƙara samun farin jini a tsakanin masu zaɓe a Zamfara saboda al’ummar karkara sun fara amincewa da kundin manufofin jam’iyyar.
Ya ce:
“ADC na da ikon lashe zaɓe a dukkan matakan siyasa a Zamfara, ko da za a gudanar da zaɓen gobe."
"Jam’iyyarmu na ƙara samun farin jini a tsakanin masu zaɓe a Zamfara saboda mutanen karkara suna da kwarin gwiwa kan kundin manufofin jam’iyyar."
A cewarsa, jam’iyyar ta riga ta kasance cikin haɗin kai, tsari da shirin tunkarar zaɓen 2027, inda “Zamfara First” yake matsayin babban ƙa’idar jagorancinta
Ya buƙaci ‘yan takarar jam'iyyar ADC da magoya bayanta a jihar su kasance masu mayar da hankali, bin doka da zaman lafiya, tare da tattaunawa kai tsaye da masu zaɓe
Garba ya kuma buƙaci jami’an jam’iyyar su guji zagi, tsokana da yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba game da batutuwan da suka shafi jam’iyyar

Kara karanta wannan
Bayan ƙalubalantar shi kan gina jami'a a Arewa, Atiku ya ce ba domin riba ya yi ba
“ADC a Zamfara za ta ci gaba da kare halastattun nasarorin ‘yan takararta, da hulɗa da hukumomin da abin ya shafa, tare da tattara magoya baya a faɗin jihar, tsarin jam’iyyar a jihar zai ci gaba da bin tanade-tanaden doka."
- in ji shi
Ya ce ajandar siyasar ADC za ta fi mayar da hankali kan tsaro, ingantaccen ilimi, kiwon lafiya da bunƙasa noma domin inganta rayuwar al’ummar Zamfara
Garba ya kara da cewa jam’iyyar za ta mayar da hankali kan samar da ayyukan yi, ababen more rayuwa, ƙarfafa mata da matasa, da kuma gaskiya da riƙon amana a mulki.
Ya ce ajandar siyasar ADC za ta fi mayar da hankali kan tsaro, ingantaccen ilimi, kiwon lafiya da bunƙasa noma domin inganta rayuwar al’ummar Zamfara
Gobara ta tashi gidan gwamnan Zamfara
An ji cewa gobara ta tashi a gidan Gwamnan Zamfara Dauda Lawal da ke GRA a Gusau da misalin karfe 7:20 na daren Talata, 1 ga watan Satumban 2026.
Hukumar kashe gobara ta jihar ta tura jami’anta zuwa gidan gwamnan domin dakile gobarar tare da hana ta bazuwa zuwa wasu sassan gidan.
Wata majiya ta ce gobarar ta shafi dakin tsaro, yayin da ba a bayyana musabbabin gobarar ko yawan barnar da ta haddasa ba.
Asali: Legit.ng
