Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Gano Abin da Ya Hana a Magance Rashin Tsaro a Najeriya
- Adewole Adebayo ya zargi wasu jami’an gwamnati da haɗa kai da ’yan bindiga domin ci gaba da yaudarar jama’a kan matsalar tsaro
- Ɗan takarar na SDP ya ce ƙara yawan kasafin tsaro yayin da sojoji ke fama da matsaloli na iya buɗe ƙofa ga almundahana
- Adebayo ya yi alkawarin fatattakar ’yan ta’adda da masu aikata laifuka tare da lalata hanyoyin tattalin arzikin da ke tallafa wa ayyukansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Adewole Adebayo, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro a Najeriya.
Adewole Adebayo ya zargi wasu jami’an gwamnati da haɗa kai da ’yan bindiga wajen ci gaba da matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta ce Adebayo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Lahadi, 6 ga watan Satumban 2026 inda ya ce rashin tsaro ya bazu zuwa sassa daban-daban na ƙasar.

Kara karanta wannan
Dan takarar shugaban kasa zai mayar da litar fetur N200, ya fadi abin da ya shirya
Ɗan takarar na SDP ya yi zargin cewa wasu jami’an gwamnati da masu aikata laifuka suna aiki tare, yayin da suke gabatar wa ’yan Najeriya wani salo daban kan abin da ke faruwa. Ya ce irin wannan yanayi ne ya sa matsalar rashin tsaro ke ci gaba da wanzuwa a ƙasar.
“Lokacin da gwamnati da ’yan bindiga suka fara shirya wasan kwaikwayo tare da yaudarar jama’a, wannan ne ya sa matsalar ta ci gaba,” in ji shi.
Kasafin tsaro na ƙaruwa
A cewar Adebayo, lamarin ya kuma samar da damar karkatar da kudaden gwamnati, musamman kudaden da ake warewa domin yaƙi da rashin tsaro.
Ya ce a wasu lokuta ana iya bayyana kudaden da aka ware domin tsaro a matsayin kuɗin fansa ko kuma kuɗaɗen gudanar da ayyukan gaggawa.
“Shi ya sa kasafin tsaro ke ƙara hawa sama, sama da sama, yayin da sojoji ke ƙara talaucewa,” in ji ɗan takarar.
Adebayo ya kuma yi zargin cewa rashin tsaro na iya zama hanyar da wasu gwamnoni ke amfani da ita wajen karkatar da makudan kudaden gwamnati ba tare da tambayoyi masu tsauri ba.
“Ta hanyar rashin tsaro ne kawai gwamna zai iya satar N500m ba tare da an tambaye shi ba, domin zai ce, ‘Na yi amfani da su wajen biyan ’yan garkuwa da mutane,’” in ji shi.
Ya yi alkawarin fatattakar ’yan ta’adda
Adebayo ya ce gwamnati na buƙatar tabbatar da cikakken iko a kowane sashe na Najeriya, domin hana ƙungiyoyin masu aikata laifuka gudanar da ayyukansu yadda suka ga dama.
Ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027, gwamnatinsa za ta ɗauki matakai masu ƙarfi wajen yaƙi da ta’addanci, rashin tsaro da kuma haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ce gwamnatinsa za ta kwato yankunan da ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka suka mamaye, tare da wargaza hanyoyin tattalin arzikin da ke taimaka musu.
“A cikin gwamnatinmu, a karon farko, gwamnati da jama’a za su haɗa kai wajen yaƙar ’yan ta’adda,” in ji shi.
Ya danganta rashin tsaro da haƙar ma’adinai

Kara karanta wannan
"Na samu labari mara dadi"; Atiku ya haska matsalar da matasa ke fuskanta a gwamnatin Tinubu
Ɗan takarar SDP ya ce yaƙi da rashin tsaro bai kamata ya tsaya kan ayyukan sojoji kawai ba, domin akwai buƙatar magance hanyoyin samun kuɗin da ke tallafa wa ayyukan masu aikata laifuka.
Ya danganta matsalar rashin tsaro da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a yankunan da ke da arzikin ma’adinai kamar zinariya, tantalite da lithium.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun sace shugaban APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa ’yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Beli da ke ƙaramar hukumar Rogo ta jihar Kano.
Hatsabiban 'yan bindigan sun kashe wani matashi tare da yin garkuwa da shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar.
Asali: Legit.ng
