2027: An Jero Wadanda bai Kamata Su Shugabanci Najeriya ba saboda Farashin Fetur

2027: An Jero Wadanda bai Kamata Su Shugabanci Najeriya ba saboda Farashin Fetur

  • Kenneth Okonkwo ya ce duk wanda ya amince yan Najeriya su ci gaba da sayen fetur kan N1,300 bai cancanci zama shugaban kasa ba
  • Mai magana da yawun yakin neman zaben Atiku ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan tsadar rayuwa da matsalar tsaro
  • Okonkwo ya ce Atiku Abubakar zai dauki matakan rage farashin fetur da inganta tsaron kasa idan ya zama shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kenneth Okonkwo, mai magana da yawun yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku Abubakar, ya ce duk wanda ke goyon bayan ci gaba da sayar da fetur kan N1,300 bai cancanci jagorantar Najeriya ba.

Ya soki gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu kan tsadar fetur, matsalar tsaro da kuma samar da wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tafka kura kurai a gwamnati, ana ganin za su jawo ya sha kaye a zaben 2027

Kenneth Okonkwo.
Kenneth Okonkwo, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar Hoto: Kenneth Okonkwo
Source: Twitter

Okonkwo ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise TV ranar Talata, 8 ga watan Satumba, 2026.

Ya ce:

"Duk wanda yake gaya muku cewa yan Najeriya za su iya biyan N1,300 kan fetur, ga farashin dizal ya haura N2,000 kan kowace lita.
"Duk wanda yake gaya wa yan Najeriya su ci gaba da biyan irin wannan kudi mutum ne azzalumi, kuma bai cancanci zama shugaban kasa a wannan kasa ba."

Okonkwo ya ba da shawara kan fetur

Okonkwo ya ce gwamnati za ta iya rage farashin man fetur da sauran man da aka tace idan tana samar da danyen mai ga matatun cikin gida kan rangwame.

Kara karanta wannan

2027: Peter Obi ya bayyana gwamna 1 da ya cancanci zama shugaban ƙasar Najeriya

Hadimin Atiku ya kuma ce samar da ingantattun kayayyakin more rayuwa ga kamfanonin mai zai taimaka wajen rage farashin.

A cewarsa:

"Dangote da kansa ya ce idan aka samar masa da dukkan danyen man da yake bukata, farashin fetur zai sauka zuwa N800 nan take."

Ya soki Tinubu kan wutar lantarki

Okonkwo ya kuma soki gwamnatin Tinubu kan yadda take tafiyar da bangaren wutar lantarki, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya zargi gwamnatin da gazawa wajen dakile yawaitar rugujewar tsarin wutar lantarki na kasa.

Ya ce:

"Tinubu ya yi yakin neman zabe da cewa idan bai samar muku da wutar lantarki ba, kada ku sake zabensa. Amma mun shaida rugujewar tsarin wutar lantarki na kasa fiye da kowane lokaci a tarihin Najeriya."
Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Facebook

Okonkwo ya dauko batun matsalar tsaro

Dangane da matsalar tsaro, Okonkwo ya zargi gwamnatin Tinubu da gazawa wajen kare yan Najeriya daga yan bindiga da yan ta'adda.

Ya ce duk gwamnatin da ba za ta iya hana sace mutane da yawa lokaci guda ba, ta gaza wajen sauke daya daga cikin manyan nauyinta.

Kara karanta wannan

"Ka yi yadda na yi," Atiku ya sake kinkimo magana mai girma kan bayanan Tinubu na Amurka

Atiku ya illar cire tallafin mai

Kun ji cewa Atiku Abubakar ya bayyana cewa cire tallafin fetur da Bola Tinubu ya yi ya kawo tsadar rayuwa, sufuri da kayan abinci.

Ya kara da cewa mutanen shugaban kasar da kuma manyan masu harkar mai ne ke morewa sakamakon cire tallafin mai amma sauran ‘yan kasuwa suna rasa abin yi.

‘Dan takaran na ADC ya ce al’umma sun ga irin salon mulkin Tinubu a rayuwarsu, yanzu ba su bukatar kara hakuri illa neman mafita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262