Matasa Sun Barke da Zanga Zanga a Faransa, ana Ta Kone Kone

Matasa Sun Barke da Zanga Zanga a Faransa, ana Ta Kone Kone

  • Dubban dalibai sun gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na Faransa, inda rikici ya barke tsakaninsu da ’yan sandan kwantar da tarzoma
  • Zanga-zangar ta haddasa katse karatu a makarantu sama da 700, yayin da aka kona shara tare da kai hare-hare kan jami’an tsaro da kadarorin makarantu
  • Hukumomin Faransa sun ce an kama mutane 1,747 a ranar Juma’a, yayin da aka samu raunuka da barna a makarantu da dama a fadin kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Paris – Rikici ya barke tsakanin ’yan sandan kwantar da tarzoma da dalibai a Faransa yayin da zanga-zangar neman inganta harkar ilimi ke kara yaduwa a kasar.

Daliban na korafin karancin malamai, cunkoson ajujuwa da kuma lalacewar gine-ginen makarantu, lamarin da ya sa zanga-zangar ta shafi birane da dama.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi Alƙawarin warware matsalar da ta fi damun yan Najeriya kan INEC da tsarin zabe

Masu zanga zanga a Faransa
Wajen da ake kone kone a Faransa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An rufe makarantu a Faransa

BBC ta wallafa cewa Ministan Shari’a na Faransa, Gérald Darmanin, ya ce zanga-zangar ta sauya daga zanga-zangar daliban sakandare zuwa rikicin da ke barazana ga zaman lafiyar jama’a.

Ya ce makarantu 735 daga cikin kusan 3,700 na kasar sun fuskanci tasirin zanga-zangar ta wata hanya, yayin da rahotanni suka nuna cewa gobara da toshe hanyoyin shiga makarantu sun faru a wurare daban-daban.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Laurent Nuñez, ya ce an kama mutane 1,747 a ranar Juma’a.

Ya ce lamarin na karkata zuwa tarzoma da rikicin birane, yana mai cewa jami’an tsaro na amfani da matakan da suka dace domin kawo karshen rikicin.

Zanga-zangar ta bazu

Zanga-zangar ta fara ne a Paris a makon da ya gabata, kafin ta bazu zuwa wasu birane kamar Montpellier, Nantes da Marseille.

A Pantin da ke wajen Paris, ’yan sanda sun fafata da masu zanga-zangar tare da kama wasu daga cikinsu bayan an jefe jami’an da abubuwa.

Kara karanta wannan

An samu matsala, mutum 3 sun mutu a gidan gwammatin jihar Neja

A Strasbourg kuwa, an yi amfani da hayaki mai sa hawaye bayan ’yan sanda sun yi fargabar cewa lamarin zai kara tsananta.

An kuma kona kwandunan shara a Rennes da Paris, yayin da wasu makarantu suka fuskanci hare-hare da barna.

An samu raunuka da barna

Ma’aikatar Ilimi ta Faransa ta ce akalla ma’aikatan makarantu 65 sun jikkata sakamakon rikicin da ake da masu zanga-zangar.

A wani lamari da ya faru a Belfort da ke arewa maso gabashin Faransa, an kama wani matashi mai shekaru 17 bisa zargin yunkurin kisan kai bayan wani jami’in ’yan sanda ya fuskanci hari.

Bidiyoyin da aka tantance sun nuna yadda wasu matasa suka bi jami’in, wanda ya fadi kasa, sannan suka rika naushinsa.

Masu zanga zanga a Faransa.
Jami'an tsaro na arangama da matasa a Faransa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al Jazeera ta wallafa cewa ’yan sanda sun wallafa hotunan wasu abubuwan da suka ce sun kwace daga hannun masu zanga-zangar, ciki har da abubuwan fashewa na gida, gatari da sauransu.

Makarantar Nelson Mandela ta Nantes ta samu barna mai yawa bayan gobara ta lalata kofar shiga ta gilashi da wasu sassan cikin makarantar. Gwamnatin yankin ta kiyasta barnar da ta haura Yuro miliyan 2.

Kara karanta wannan

An kai Dangote kotun Kenya, an hana kawo masa cikas wajen gina matatar mai

Dalilan zanga-zangar Faransa

Daliban da ke zanga-zangar sun ce suna neman karin malamai, rage cunkoso a ajujuwa da gyara gine-ginen makarantu.

Wata daliba mai shekaru 16 mai suna Lola ta ce rufe makarantar tasu sakamakon zanga-zangar ya nuna cewa dalibai sun cimma wani bangare na abin da suke nema.

Ta kuma zargi ’yan sanda da kara dagula lamarin ta hanyar amfani da karfi da hayaki mai sa hawaye.

A gefe guda, Ministan Ilimi Édouard Geffray ya ce wasu mutanen da ba dalibai ba sun shiga cikin zanga-zangar tare da kara dagula lamarin.

An rage kudin mai a Jamus

A wani labarin, mun ruwaito cewa farashin man fetur a Jamus ya fara saukowa bayan gwamnati ta fara aiwatar da tallafin da aka tanada domin rage tasirin tashin farashin makamashi da rikicin Gabas ta Tsakiya ya haddasa.

Farashin fetur ya ragu da kusan cent 14 zuwa Yuro 2.06 kan lita, yayin da dizal ya ragu da cent 15 zuwa Yuro 2.20 kan lita, bisa bayanan kungiyar masu ababen hawa ta ADAC.

Sai dai wasu masu ababen hawa sun ce rangwamen bai wadatar ba, inda wata mazauniyar Frankfurt mai suna Andrea Hoecker ta bayyana cewa matakin taimako ne na dan lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng