Mutanen da Suka Ce APC Ta Dauko Su Haya a Taron Kano Sun Yi Fallasa
- Wasu mazauna Kano da suka halarci wani aikin yakin neman zaɓen APC sun nuna rashin gamsuwa bayan an ce an ba su N3,000
- Wasu daga cikin mahalartan sun ce kudin bai isa ya biya kuɗin mota da suka kashe wajen zuwa wurin taron ba balle na komawa
- Ɗaya daga cikin mutanen ya yi gargadin cewa za su daina halartar ayyukan yakin neman zaɓen APC idan aka ci gaba da ba su irin kudin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – Wasu magoya bayan jam’iyyar APC da suka halarci wani aikin wayar da kan jama’a a Kano sun koka kan N3,000 da ake zargin an ba su bayan sun kammala taron.
Mahalartan, waɗanda aka gan su sanye da rigunan APC, sun bayyana rashin gamsuwarsu ne a wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa korafin ya biyo bayan wani gagarumin aikin tattara magoya baya da APC ta gudanar a Kano, inda jam’iyyar ta karɓi mambobi sama da 136,000.
Kudin da aka ce an ba su
Ɗaya daga cikin mutanen ya ce wasu daga cikin mahalartan sun ciwo bashi domin samun kuɗin mota kafin su zo wurin taron, amma daga baya aka ba su N3,000 kacal.
Ya ce:
“Idan kuka ci gaba da ba mu N3,000 a yakin neman zaɓen APC, ba za mu sake zuwa ba. Wasu daga cikinmu mun ciwo bashi domin kuɗin mota mu zo wurin taron, amma N3,000 kawai ake ba mu.”
Mutanen sun bayyana rashin jin daɗinsu yayin da suke tattauna kan kudin da aka ba su, inda ɗaya daga cikinsu ya yi gargadin cewa irin wannan adadin na iya hana wasu sake halartar ayyukan jam’iyyar.
Barazana daina zuwa taro
Bayan bayyana rashin gamsuwarsu, ɗaya daga cikin mahalartan ya yi gargadin cewa ba za su sake komawa ayyukan yakin neman zaɓen APC ba idan aka ci gaba da ba masu halarta irin wannan adadin.
Lamarin ya faru ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙara ƙaimi wajen tattara magoya baya da gudanar da taruka gabanin babban zaɓen 2027.

Source: UGC
APC na ci gaba da ƙarfafa tsarin siyasarta a Kano, yayin da shugabannin jam’iyyar ke kira ga ƙarin haɗin kai da tallafa wa ‘yan takararta tun daga matakin ƙasa.
Ga bidiyon mutanen da shafin Citizens Mirror ya wallafa a X:
Mutanen da APC ta karba a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar APC a Kano ta karɓi Sanata Rufa’i Sani Hanga da Kabiru Ibrahim Gaya, da Shugaban tsagin NNPP.
An karɓi waɗanda suka sauya sheka ne yayin ƙaddamar da ƙungiyoyin yakin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu a Kano gabanin babban zaɓen 2027.
Daga cikin fitattun ‘yan siyasar da suka koma APC akwai Mataimakin Shugaban jam’iyyar NDC a Kano, Hon Ali Datti Yako, tare da wasu mambobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar.
Asali: Legit.ng

