Siyasar 2027 Ta Dauki Zafi, an Kai Korafin Atiku gaban EFCC kan Zargin Badakala

Siyasar 2027 Ta Dauki Zafi, an Kai Korafin Atiku gaban EFCC kan Zargin Badakala

  • Jigon APC ya bukaci EFCC ta binciki zarge-zargen badakalar kudi da ake dangantawa da dan takarar ADC Atiku Abubakar
  • Eta ya ce binciken bai kamata ya zama farautar siyasa ba, yana mai cewa babu wani dan siyasa da ya fi karfin doka
  • Ya bukaci hukumomin yaki da cin hanci su binciki korafe-korafe da hujjoji ba tare da tsoro ko son rai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban APC na shiyyar Kudu maso Kudu, Ntufam Hilliard Eta, ya bukaci hukumomin yaki da cin hanci su binciki Atiku Abubakar.

Eta ya bukaci Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC da sauran hukumomin da suka dace su binciki zarge-zargen.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tafka kura kurai a gwamnati, ana ganin za su jawo ya sha kaye a zaben 2027

Jigon APC ya bukaci EFCC ta binciki Atiku
Jami'an hukumar EFCC da Atiku Abubakar. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission, Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Muhammadu Buhari House da ke Abuja, inda ya ce babu wani dan siyasa da ya fi karfin doka, cewar The Nation.

Yadda jigon APC ke son a binciki Atiku

Eta, ya ce kiran nasa ya samo asali ne daga bukatar adalci iri daya, ba farautar siyasa ba.

Ya ce rike da mukamin gwamnati bai kamata ya kare kowa daga bincike ba, domin dole ne hukumomi su duba zarge-zargen da ake gabatarwa.

Eta ya ce ya kira taron manema labarai ne saboda akwai lokutan da ya kamata kishin siyasa ya ba da dama ga ka’idar rikon amana.

Ya ce Najeriya ba za ta iya gina ingantacciyar dimokuradiyya ba idan ana amfani da rikon amana ta hanyoyi daban-daban.

Eta ya jaddada cewa mukamin gwamnati bai kamata ya zama garkuwa daga bincike ba, kuma burin siyasa bai kamata ya sa hukumomi su kau da kai ba.

Kara karanta wannan

Dalung ya jefawa Christopher Musa tambayoyi kan zargin Nasir El Rufa'i

Ya yi nuni da wasu tsofaffin batutuwa da kuma sabbin korafe-korafe, ciki har da takardar da aka gabatar wa EFCC ranar 1 ga Satumba.

A cewar Eta, takardar ta bukaci a sake bude binciken zarge-zargen laifukan kudi da suka samo asali tun daga shekarun 2005 zuwa 2006.

Ana neman sake tono zargin badakala kan Atiku
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Sai dai ya bayyana cewa kiran binciken ba yana nufin an tabbatar da Atiku da laifi ba, domin zarge-zargen ba a tabbatar da su a kotu ba.

Kai'idojin da ya kamata hukumomi su bi

Ya ce ya kamata hukumomin shari’a su bi ka’idojin da suka dace wajen gudanar da binciken, maimakon a yanke hukunci bisa ra’ayin jama’a.

Eta ya ce ba ya neman a samu hukuncin Atiku a gaban kotun ra’ayin jama’a, sai dai a gabatar da hujjojin ga kotun doka.

Ya kuma ce idan hujjojin ba su wadatar ba, ya kamata a sanar da ’yan Najeriya, amma idan hujjoji sun tabbatar da laifi, doka ta yi aikinta, cewar Daily Post.

Eta ya bukaci hukumomin yaki da cin hanci su gudanar da ayyukansu ba tare da nuna bambanci ba, ko da mutum yana wace jam’iyya.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya jero masu amfana da cire tallafin man fetur da Tinubu ya yi

Atiku ya kalubalanci Tinubu kan zargin cin hanci

Mun ba ku labarin cewa Atiku Abububakar ya buƙaci gwamnati ta fito da kwararan hujjoji a kansa maimakon sake dawo da tsofaffin zarge-zarge.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa bai taɓa jagorantar aiwatar da aikin wutar lantarki na $16bn a baya.

Maimakon haka, ya buƙaci Bola Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya bayanin inda kuɗin da aka tara daga cire tallafin fetur suka shige.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.