Wata Sabuwa: An Tono Babbar Badakala da Ta Shafi Atiku, Ana Neman Gurfanar da Shi a Kotu
- Ehiozuwa Agbonayinma ya bukaci hukumar EFCC ta sake bude bincike kan wasu zarge-zargen almundahanar kudi da suka shafi Atiku Abubakar
- Lauyoyin tsohon dan Majalisar sun bai wa hukumar EFCC wa'adin kwanaki 14 ta dauki mataki kan bukatar
- Sun ce za su dauki matakin shari'a idan hukumar ta gaza yin abin da ya dace kan tsohon mataimakin shugaban kasar cikin wa'adin da aka bayar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Tsohon dan majalisar wakilai, Ehiozuwa Agbonayinma, ya bukaci Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Tu'annati (EFCC) ta sake bude bincike tare da gurfanar da Atiku Abubakar kan wasu zarge-zarge.
Atiku shi ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC kuma ya rike kujerar mataimakin shugaban kasa daga 1999 zuwa 2007.

Source: Facebook
Agbonayinma ya gabatar da bukatarsaga EFCV ne ta hannun lauyansa, Hannibal Uwaifo, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Lauyan ya bai wa hukumar EFCC wa'adin kwanaki 14 domin daukar mataki kan bukatar.

Kara karanta wannan
Atiku ya nuna yadda kalaman IPMAN suka 'kunyata' Tinubu kan dawo da tallafin fetur a Najeriya
Dalilin bukatar sake bude binciken
A wata wasika mai kwanan watan 27 ga watan Agusta, wadda hukumar EFCC ta karba ranar 1 ga watan Satumba, Uwaifo ya ce bukatar ta samo asali ne daga wani bincike da EFCC ta gudanar kan zarge-zargen da suka shafi Atiku.
Rahoton ya shafi lokacin tsakanin shekarar 2005 zuwa 2006, lokacin da Atiku yake mataimakin shugaban kasar Najeriya.
A cewar wasikar, rahoton ya kunshi wasu zarge-zargen da suka hada da almundahana, halatta kudaden haram da sauran manyan laifuffukan kudi da ake alakanta su da tsohon mataimakin shugaban kasar.
Zargin EFCC ba ta gurfanar da Atiku ba
Lauyoyin Agbonayinma sun ce a lokacin, EFCC ta nuna cewa za ta gurfanar da Atiku bayan ya bar mukaminsa. Sai dai sun yi zargin cewa ba a taba gurfanar da shi kan wadannan batutuwa ba.
Lauyoyin sun bayyana rashin daukar mataki a matsayin abin da suka kira babban saba wa dokar da ta kafa hukumar EFCC.

Kara karanta wannan
Atiku ya ɗauko batun abin da ya faru da Tinubu a 1993, ya aika sako fadar shugaban kasa
An dauko rahoton majalisar Amurka
Wasikar ta kuma yi nuni da wani rahoto da Kwamitin Bincike na Majalisar Dattawan Amurka ya fitar, a ranar 4 ga watan Fabrairun 2010.
Lauyoyin Agbonayinma sun yi zargin cewa rahoton Amurka ya kunshi wasu manyan zarge-zarge da suka shafi halatta kudaden haram da sauran laifuffukan kudi da ake alakanta su da Atiku.
Sun bukaci hukumar EFCC ta sake bude kundin bincike kan rahoton 2006 da kuma rahoton Majalisar Dattawan Amurka na 2010.
A cewar wasikar, Agbonayinma ya ce sake bude batun zai nuna shirye-shiryen hukumar EFCC na yaki da cin hanci da rashawa, har ma idan wadanda ake zargi manyan mutane ne.
Wasikar ta ce:
“Wnda muke karewa ya yi imanin cewa shugabancin EFCC na yanzu yana da dukkan karfin da ake bukata domin taimakawa Najeriya fita daga matsayin da take ciki na yawan cin hanci da rashawa.”
Lauyoyin Agbonayinma sun gargadi hukumar EFCC cewa idan ta gaza daukar mataki cikin kwanaki 14 da karbar wasikar, za su dauki matakin shari'a.
Asali: Legit.ng