Dalung Ya Jefawa Christopher Musa Tambayoyi kan Zargin Nasir El Rufa'i

Dalung Ya Jefawa Christopher Musa Tambayoyi kan Zargin Nasir El Rufa'i

  • Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya fuskanci kira da a fito da hujjoji kan zargin da ya yi wa tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, na hannu wajen kisan al’ummar Kudancin Kaduna
  • Wannan zargi ya sake jawo ce-ce-ku-ce, musamman bayan tsohon Janar Danjuma Ali-Keffi ya kalubalanci Musa da ya gabatar da hujjojin da ke tabbatar da ikirarin nasa
  • Solomon Dalung ya ce irin wannan zargi ya yi nauyi matuka, don haka bai kamata a bar shi a matsayin wata takaddamar siyasa ko ce-ce-ku-cen kafafen sada zumunta kawai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wani sabon martani ya bukaci Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya fito da cikakkun bayanai kan zargin da ya yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na cewa ya shirya kisa a Kudancin Kaduna da gangan.

Kara karanta wannan

Zargin El Rufai: Hadimin Uba Sani ya kare Janar Christopher Musa

Dalung ya ce ya saurari kalaman Musa a baya-bayan nan a hankali, yana mai cewa bai kamata ‘yan Najeriya su dauki lamarin a matsayin wata takaddamar siyasa tsakanin manyan ‘yan Arewa biyu ba.

Christopher Musa, Solomon Dalung Nasir El-Rufa'i
Nasir El-Rufa'i a tsakiyar Solomon Dalung da Christopher Musa. Hoto: Bello El-Rufa'i|Solomon Dalung|GEN CG Musa
Source: Facebook

Solomon Dalung ya yi wa ministan tsaron tambayoyi ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin.

Yadda rikicin Kaduna ya fara

Dalung ya ce tarihin rikicin Kaduna bai fara ne a shekarar 2015 lokacin da El-Rufai ya zama gwamna ba.

Ya kawo misalan rikicin Kafanchan na 1987, Zangon Kataf na 1992, rikicin Shari’a na 2000 da tashin hankalin bayan zaben 2011, yana mai cewa rikice-rikicen sun samo asali ne daga abubuwa da suka hada da filaye, kiwo, iyakoki da sauransu.

Sai dai ya jaddada cewa wannan ba yana nufin a wanke El-Rufai daga alhakin abubuwan da suka faru a Kaduna tsakanin 2015 zuwa 2023 ba.

Ya ce dole ne a duba yadda ya tafiyar da matsalolin da ya gada, amma akwai babban bambanci tsakanin cewa manufofin El-Rufai ko gazawarsa sun taimaka wajen kara rikici da kuma zargin cewa ya shirya kisan al’ummar Kudancin Kaduna.

Kara karanta wannan

‘Mulkinsa ya shafi kowa a Kaduna': Jigon APC ya kare kalaman minista kan El Rufai

Kwamitin Agwai ya binciki rikicin

Dalung ya tunatar da cewa bayan El-Rufai ya zama gwamna a 2015, ya kafa kwamitin da Janar Martin Luther Agwai ya jagoranta domin binciken rikicin Kudancin Kaduna.

Agwai, wanda ya fito daga Kagoro a Kudancin Kaduna, ya taba zama Babban Hafsan Sojojin Kasa sannan daga bisani ya zama Shugaban Hafsan Tsaron Najeriya.

Ya ce binciken kwamitin ya nuna cewa rikicin yana da dogon tarihi, wanda ya shafi rikicin bayan zaben 2011 da kuma rikice-rikicen manoma da makiyaya da batun ‘yan asali da mazauna yankin.

Kwamitin ya kuma bayar da shawarwari da suka hada da tattaunawa, sulhu da samar da hanyoyin sasanta bangarorin da abin ya shafa.

Nasir El-Rufa'i a Kaduna
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i. Hoto: Bello El-Rufa'i
Source: Facebook

Tambayar Dalug da Janar Musa

Ya tambayi lokacin da Musa ya fara samun irin wannan bayanin, wanda ya sanar da shi, ko an shigar da shi cikin bayanan sirrin soja, da kuma ko an taba gabatar da shi ga shugaban kasa ko mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Kara karanta wannan

Dan Majalisa ya kai ƙorafi gaban shugaban Amurka kan abin da ake wa Tinubu a Najeriya

Ya ce idan Musa ya taba kai rahoton amma aka yi watsi da shi, ‘yan Najeriya ma suna da hakkin sanin hakan.

Dalung ya kuma tabo batun tikitin Musulmi da Musulmi da El-Rufai ya yi amfani da shi a Kaduna.

El-Rufai ya zabi Hadiza Balarabe, Musulma daga Kudancin Kaduna, a matsayin mataimakiyarsa a shekarar 2019 kuma ya ci gaba da rike ta a 2023.

Sai dai Dalung ya ce idan matsalar Musa ta samo asali ne daga tikitin Musulmi da Musulmi, to ya kamata a bayyana dalilin da ya sa irin wannan tsari bai zama matsala ba a gwamnatin tarayya ta Tinubu.

Girman dajin Sambisa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya kare kokarin gwamnati na yaki da rashin tsaro, yana mai cewa girman wuraren da ‘yan ta’adda ke fakewa na kawo cikas ga ceto jama'a.

Musa ya ce jami’an tsaro na ceto mutanen da aka yi garkuwa da su akai-akai, amma ‘yan ta’adda kan shiga manyan dazuzzuka kafin jami’an tsaro su gano inda suke, inda ya ce dajin Sambisa yana da fadin da ya kai Belgium.

Ya kuma bayyana cewa ‘yan ta’adda kan shiga daji kafin labarin satar mutane ya isa ga jami’an tsaro, lamarin da ke kara tsawaita lokacin da ake bukata wajen bin sawunsu da kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng