Jamhuriyar Nijar Ta Faɗi Ƙasashen da Take Zargi da Yunkurin Yi Mata Juyin Mulki
- Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta zargi Faransa da hannu a yunkurin juyin mulkin da aka yi, amma Faransa ta musanta zargin
- Sojojin da suka yi bore sun kwace wasu wurare a Yamai, ciki har da filin jirgin sama, kafin jami’an tsaro su dakile su
- Nijar ta ce ta tattara shaidu kan lamarin kuma tana iya kai karar masu hannu a gaban kotunan kasa da kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Niamey, Niger - Gwamnatin Nijar ta zargi Faransa da hannu a wani yunkurin juyin mulki da aka shirya domin hambarar da gwamnatin mulkin soja.
A baya, Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu sojoji sun bar wuraren da suke aikin yaki, sannan suka fara abin da hukumomi suka bayyana a matsayin bore.

Source: Facebook
Harin da aka kai a Jamhuriyar Nijar
Tsakanin ranakun 28 da 29 ga watan Agusta, sojojin sun kwace iko da wasu muhimman wurare, ciki har da filin jirgin saman Diori Hamani da sansanin jiragen sama na 101, cewar Premium Times.
Har ila yau, sojojin sun yi yunkurin kutsawa cikin yankin fadar shugaban kasa mai tsananin tsaro.
Sai dai bayan shafe sa’o’i ana fafatawa, jami’an tsaro sun fatattaki sojojin da suka yi bore, inda aka kama ko kashe wasu daga cikinsu.
An zargi Faransa kan yunkurin juyin mulki
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa gwamnatin Nijar ta sanar a ranar Juma’a, ta gidan talabijin na kasa, cewa bincikenta ya gano cewa wata hanyar sadarwa ce ta taimaka wa bore.
Gwamnatin ta ce Faransa ce ke jagorantar mutanen da ake zargi da hannu wajen shirya harin.
Gwamnatin mulkin sojan ta kuma ce ta tattara “manyan shaidu” kan harin, kuma Nijar na da damar kai lamarin gaban kotunan kasa da kasa.
A cewar Sahel Alerte, wata kafar da ke bibiyar yanayin tsaro a yankin, Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean-Noël Barrot, ya ce babu “niyya ko wata hanya” da za ta bai wa Faransa damar kai harin soja kan Nijar.
Zargin ya zo ne kwanaki kadan bayan wani babban kwamandan sojan Nijar ya yi ikirarin cewa kasashe makwabta sun goyi bayan bore.
Roger Gabriel, wani kyaftin na sojan Nijar, ya bayyana a gidan talabijin na gwamnati, inda ya zargi wasu mutane da hannu wajen harin.

Source: UGC
Najeriya ta nesanta kanta daga zargin
Gwamnatin Najeriya ma ta fitar da sanarwa, inda ta nesanta kanta daga yunkurin juyin mulkin da aka yi a Nijar.
Karamin Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Sola Enikanolaiy, ya ce akwai “zarge-zargen karya da na mugun nufi” da ke cewa Najeriya da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS, sun goyi bayan bore.
Dangantakar Nijar da Faransa ta tabarbare
Dangantakar Nijar da tsohuwar kasar da ta yi mata mulkin mallaka, Faransa, da kuma kawayenta na yankin, ta tabarbare matuka tun bayan da sojoji suka kwace mulki a watan Yulin 2023.
Juyin mulkin ya haifar da rugujewar alakar diflomasiyya tsakanin kasashen, inda gwamnatin mulkin sojan Nijar ta bukaci Faransa ta janye dakarunta.
Hukumomin Nijar sun magantu kan yunkurin juyin mulki
An ji cewa Jami'an tsaron Nijar tare da taimakon dakarun kasar Rasha sun samu nasarar murkushe yunkurin juyin mulki a Niamey.
Shugaban mulkin sojan kasar, Abdourahamane Tchiani, yana ci gaba da rike madafun iko duk da luguden wuta da aka sha.
Yanayin fargabar da ake ciki na samar da dama ga kungiyoyin 'yan ta'adda na kara bazuwa a cikin Jamhuriyyar Nijar.
Asali: Legit.ng


