Tompolo Ya Shigo Arewa da Motocin Tallan Tinubu, Ya Dura a Katsina
- Attajirin Kudancin Najeriya da aka sani da Tompolo, ya kaddamar kungiyar tallata Bola Tinubu a jihar Katsina domin tara goyon bayan jama’a ga sake zabensa a 2027
- Tompolo, wanda ya kafa kuma ke jagorantar kungiyar, ya zabi Katsina a matsayin jihar farko da za a fara kaddamar da shirin a Arewa, inda aka nada shugabanni
- An raba motoci 34 na yakin neman zabe ga masu kula da kananan hukumomi 34 domin taimakawa wajen gudanar da yakin neman goyon bayan Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Katsina – Attajirin da aka fi sani da Tompolo ya kaddamar da PBAT Door-to-Door Movement a jihar Katsina, a wani yunkuri na kara tara goyon bayan jama’a ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaben 2027.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a People’s Square da ke Katsina, inda aka nada masu kula da kungiyar a kananan hukumomi 34 tare da mika musu motocin yakin neman zabe.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa taron ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki na APC a Katsina da ma Najeriya baki daya.
An raba motocin tallan Tinubu
Hadimin gwamnan Katsina, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook cewa a yayin bikin, an raba motoci 34 ga masu kula da kungiyar a kananan hukumomin jihar Katsina 34.
An ce motocin za su taimaka wajen karfafa ayyukan wayar da kan jama’a da kuma tattara goyon bayan Shugaba Tinubu a matakin karkara.
Maganar Gwamna Dikko Radda
A nasa jawabin, Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya tabbatar wa Shugaba Bola Tinubu da goyon bayan jihar Katsina ga yunkurinsa na sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Radda ya bayyana Katsina a matsayin jihar APC, yana mai cewa dukkan zababbun 'yan siyasa a jihar mambobin jam’iyyar ne kuma tsarin jam’iyyar ya kasance dunkule a kananan hukumomi 34.
Tsohuwar alakar Tinubu da Arewa
Gwamna Radda ya danganta alakar Tinubu da Katsina da dadadden tarihi na hulda tsakanin shugaban da wasu fitattun shugabannin siyasar Arewa.
Ya kuma tuna da rawar da Tinubu ya taka a tsarin siyasar da ya kai ga nasarar marigayi Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2015.
Radda ya yaba wa Tompolo bisa zabar Katsina a matsayin jihar farko a Arewa da aka kaddamar da wannan yunkuri na yakin neman goyon bayan Tinubu.
Kiran Akpabio ga 'yan Arewa
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya fara neman goyon bayan sake zaben Shugaba Bola Tinubu a 2027, inda ya bukaci matasan Arewa su goyi bayan sauye-sauyensa.
Akpabio ya yi wannan kiran ne a Abuja yayin da ya karbi wata tawaga mai manyan mukamai daga Northern Ethnic Groups Assembly, inda ya kare cire tallafin man fetur da sauye-sauyen Tinubu.
Ya bayyana matakan a matsayin masu radadi amma wajibi domin sake fasalin tattalin arzikin Najeriya, yana mai cewa sauye-sauyen sun fara haifar da wasu sakamako masu kyau ga ‘yan kasar.
Asali: Legit.ng

