Tirkashi: EFCC Ta Fara Farautar Babbar Jagora a Kungiyar Yakin Neman Zaben Tinubu
- Hukumar EFCC ta ayyana neman Halimat Adenike Tejuosho, shugabar matan ƙungiyar City Boy Movement ruwa a jallo kan zargin damfara
- Ana zargin Tejuosho da karɓar kuɗaɗe a hannun mutane ta hanyar yin amfani da takardun bogi tana yi musu alkawarin ba su ayyukan gwamnati
- Bayan sanarwar EFCC, ƙungiyar CBM da ke yakin neman zaben Shugaba Bola Tinubu ta dauki matakin gaggawa kan Halimat domin kare kanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta fitar da sanarwar neman Halimat Adenike Tejuosho, shugabar mata a kungiyar yakin neman zaben Tinubu, CBM.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Litinin, ta bayyana cewa ana neman Tejuosho ne don amsa tambayoyi game da zargin zamba da karɓar kuɗaɗe ta hanyar yaudara.

Source: Facebook
EFCC na farautar Halimat Adenike Tejuosho
Tejuosho, wadda ƴar asalin jihar Legas ce, tana zaune ne a unguwar Maitama Extension da ke Abuja, kamar yadda EFCC ta wallafa sanarwa a shafinta na Facebook.
Hukumar EFCC ta yi kira ga duk wanda yake da bayanan da za su kai ga kamo Halimat Adenike Tejuosho da ya tuntuɓi ofisoshinsu da ke faɗin ƙasar nan ko kuma tashar ƴan sanda mafi kusa.
Sanarwar ta ce:
“Duk wanda yake da sahihan bayanai kan inda take, ya tuntuɓi hukumar a ofisoshinta na Ibadan, Uyo, Sakkwato, Maiduguri, Benin, ko kuma ta lambar waya 08093322644.”
Zargin da ake yi wa Halimat Tejuosho
Wannan ba shi ne karon farko da Tejuosho ke shiga hannun hukuma ba, kamar yadda rahoton jaridar The Cable ya nuna.
A watan Yunin 2025, hukumar EFCC ta taba yi mata tambayoyi bayan korafe-korafen da aka samu na cewa tana karɓar kuɗi a hannun mutane da sunan ba su aikin gwamnatin tarayya.
Ana zargin Tejuosho, wadda ita ce mamallakiyar kamfanin Haleems Integrated Services Limited, da amfani da takardun naɗin aiki na bogi don yaudarar mutane.
Duk da cewa an taba ba ta belin gudanarwa a wancan lokacin yayin da ake ci gaba da bincike, sabon matakin na EFCC ya nuna cewa al'amarin ya ɗauki sabon salo.

Source: Facebook
Kungiya yakin Tinubu ta dakatar da Halimat
Jim kaɗan bayan sanarwar EFCC, ƙungiyar City Boy Movement ta fitar da nata jawabin na dakatar da Tejuosho daga muƙaminta na shugabar mata ta shiyyar kudu maso yamma.
Ƙungiyar ta bayyana cewa wannan mataki ya zama dole domin kare kima da martabar ƙungiyar a idon duniya.
A cikin wata sanarwa, ƙungiyar ta jaddada cewa:
“Wannan mataki an ɗauke shi ne don tabbatar da cewa bincike ya gudana ba tare da katsalandan ko cikas ba. Muna da manufar rashin amfani da duk wani abu da zai kawo nakasu ga mutuncin ƙungiyarmu.”
An kaddamar da City Boy Movement
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'dan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Seyi Tinubu, ya sake ba yan Najeriya hakuri kan shugabancin mahaifinsa.

Kara karanta wannan
2027: An fara tsoron sanatan APC zai raunana aikin Tinubu bayan gana wa da Atiku Abubakar
Wannan na zuwa ne yayin da Seyi Tinubu ya fara gina wata tafiyar siyasa ta matasa a fadin Najeriya, City Boy Movement, domin zaben shekarar 2027.
Wannan na zuwa ne yayin da Seyi Tinubu ya fara gina wata tafiyar siyasa ta matasa a fadin Najeriya baki daya domin zaben shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

